Gwamnatin Katsina Ta Horas da Yan Mata dama da 450 Sana’o’i
Gwamnatin jihar Katsina ta horar da ‘yan mata dama da 450 sana’o’i daban-daban domin dogaro da kai a jihar.
Daga cikin sana'o'in sun hada da dinki da sabulu da sauran sana’o’in hannu da sashen ci gaban yara mata a ofishin gwamna ya yi, sun kuma samu kayayyakin fara aiki da kudade a matsayin tallafi.
Gwamna Umar Dikko Radda wanda ya kasance...
Hasumiyyar Gobarau: Ginin Da Ya Haura Shekara 600 A Katsina
Hasumiyar Gobarau na daya daga cikin dogayen gine-ginen tarihi a Jihar Katsina, kuma an yi has ashen cewa an gina ta wajen shekaru sama da 600 da suka gabata. An gina hasumiyar da irin tsarin gine-ginen Mali.
Tarihi ya tabbatar da cewa an gina ta ne domin bauta, kuma daga bisani hasumiyyar ta dauki gurbin tsare garin daga mahara, ta...
‘Yan sanda sun kama wani mutum da yayi yunkurin kashe matarsa da taɓarya a Bauchi
'Yan sanda sun kama wani mutum da yayi yunkurin kashe matarsa da taɓarya a Bauchi
Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta cafke wani dan kasuwa kan yunkurin kashe matarsa don ya samu damar sayar da talabijin dinsu ya kara jari a shagonsa a Jihar Bauchi.
Magidancin mai shekaru 35 ya shiga hannu ne bayan ya yi amfani da tabarya wajen dukan...
Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Aikewa Da Jami’an Tsaro Zuwa FUDMA
Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin tura karin jami’an tsaro domin kare Jami’ar Tarayya ta Dutsima (FUDMA), da ke Katsina domin fara gudanar da karatu.
Da yake zantawa da manema labarai a makarantar, mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, ya ce mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribado ya bayar da umarnin a kara tura jami’an...
Hukumar NDLEA ta kai wani samame ta kama ango da abokan sa 25 a Katsina
Daga Muhammad Kabir, Katsina
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Katsina, sun dakile wata gasar shan miyagun kwayoyi da aka gudanar kafin a ɗaura wani aure a unguwar Shola Quarters a cikin birnin jihar.
Majiyar Jaridar Taskar Labarai ta ruwaito jami'an sun cafke matasa 25 da ke gudanar da shagulgulan bikin na shan...
Gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 15 yan jihar Katsina
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da sakin fursunoni 15 daga cibiyar da ake tsare dasu ta Malumfashi da ke Katsina a jiya Asabar.
Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kula da gidagen gyaran hali na Najeriya, Mista Haliru Nababa, ya bayyana hakan a yayin wani taro, cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya taimaka wajen sakin mutanen.
Nababa, wanda ya...
An sake gurfanar da Tinubu a kotun koli kan zaben 2023
An sake gurfanar da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a gaban kotun koli bisa zarginsa da gabatar da kansa a matsayin shugaban kasa ba bisa ka’ida ba, lokacin da ake jiran hukuncin kotu kan gudanar da zaben shugaban kasa na 2023.
Dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Cif Albert Ambrose Owuru ne ya shigar da wannan kara, inda ya...
Yan sanda sun ceto mutane 69 da aka yi garkuwa da su a Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Talata gata gabata ta ce ta ceto mutane 69 da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar.
Wannan wani bangare ne na nasarori da rundunar ta samu daga Watan Nuwamba 1 ga wata zuwa 30 ga wata na 2023.
Rundunar...
Jami’an Sibil Difens Sun Kama Matashin Da Ya Yi Wa ’Yar Masoyiyarsa Fyade
Wani matashi da ya yi wa ’yar masoyiyarsa fyade ya shiga hannun Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a garin Abeokuta na JIhar Ogun.
Matashin mai shekaru 35 ya yi wa yarinyar fyade ne alhali ya kasance yana soyayya da mahaifiyarta.
Kakakin Hukumar NSCDC na Jihar Ogun, Dyke Ogbonna, ya ce iyalan yarinyar ne suka kawo wa hukumar kara,”bayan bincike kuma wanda ake...
An samu asarar rayukan masu haƙar ma’adanai a Zamfara.
Aƙalla masu aikin haƙar ma'adanai mutum uku ne suka rasu yayin da wasu mutum 11 suka samu raunuka sakamakon ruftawar wani ramin haƙar ma'adinai a Dan Kamfani da ke ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
A cewar wani ganau da ke aiki a kewayen yankin, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma.
Wani ganau wanda...