Daga Misbahu Ahmad
@ katsina city news
Da misalin ƙarfe biyu na ranar lahadi, 04-09-2022 ƴan bindiga suka kawo hari cikin garin Batsari, ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Maharan dake kan babura guda biyar kowannen su da goyo, sun shigo garin ne ta hanyar Yasore suka ratsa unguwar katoge, kusa da makarantar ƴan mata watau kwamuniti sakandire (CGDSS) Batsari.
yan bindigar sun rika harbi kan mai uwa da wabi, suka biyo titin tashar Ruma (Tsohuwar hanyar Ruma), suka tsaya daidai masallacin Malam Salisu Wagini suna kabbara suna harba bindigu.
Ƴan bindigai dake sanye da kakin sojoji, daga nan sukayi yamma suka nufi wajen masallacin katoge. lokacin da suke ƙoƙarin fita gari sun kutsa kai cikin gidan wani bawan Allah mai suna Abdullahi Haruna wanda ake yima laƙabi da folis, inda suka fito da shi ta tsiya-tsiya sukace ya hau babur su tafi da shi, yaƙi ya hau, nan take suka bindige shi har lahira, sannan suka wuce hankalin su kwance.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email: katsinacitynews2@gmail.com