BARA GURBIN ‘YAN JAM’IYYAR PDP NE KAƊAI KE CANZA SHEƘA ZUWA WASU JAM’IYYU IN JI MAƘARFI

0

Daga Bishir Sulaiman

Tsohon shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP Sanata Ahmed Maƙarfi, ya bayyana cewa bare gurbin ‘yan jam’iyyar ne, da ke ɓata wa jam’iyyar suna, su ne ke fita daga jam’iyyar.
fitar irin waɗannan mutane, a jam’iyyar zai bai wa mutanan kirki masu bin doka da oda zama cikin kwanciyar hankali a PDP

Ya kuma tabbatar wa da ‘yan ƙasar nan cewa muddin suka dawo kan mulki a shekarar 2019, za su ƙoƙarta wajen fitar da jama’a halin ƙaƙanikayin da ƙasar ke ciki.
Ya bayyana haka ne, a wajen taron jam’iyyar na yankin Arewa maso yamma da aka gudanar a harabar sakatariyar jam’iyyar ta jihar Katsina a ranar asabar.

A makamanciyar wannan tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya buƙaci Al’ummar ƙasar nan da su dage su mallaki katin zaɓe, domin da shi ne kaɗai, za a samu damar zaɓen shuwagabannin da suke so, a zaɓuka masu zuwa na shekarar 2019.
Ya ƙara da cewa, duk yadda aka kai ƙololowar san mutum ya samu nasara, in ba a mallaki katin zaɓe ba, babu abin da za a iya masa, dangane da kaɗa masa kuri’ah.

See also  Wa Ya Kamata Jam’iyyar PDP Ta Tsayar Takarar Gwamna A Katsina?

Ya kuma buƙaci ‘yan jam’iyyar da su ƙara ƙoƙari wajen wayar da kan jama’a muhimmancin mallakar katin zaɓe.

Da ya ke magana a wurin taron shugaban Jam’iyyar adawar ta PDP na ƙasa Uche Secondus, ya bayyana jin daɗinsa ga jama’a game da yadda suka jajirce wajen fitowa da nuna goyan bayansu ga jam’iyyar, wanda hakan ya tabbatar masa har yanzu jam’iyyar tana da ƙwarin guiwar samun nasarar lashe zaɓɓuka masu zuwa a jihar Katsina dama ƙasa baki ɗaya a shekara ta 2019.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wasu wakillan jam’iyyu na PDM da APGA da kuma APC sun sauya sheƙa ya zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a wurin gudanar da taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here