Wai Duniya Saura Shekara … Ta Qare?

0

Daga Danjuma Katsina

A binciken masana ilmin taurari da sararin samaniya [ASTOROMANAS] sun ce wannan duniyar ta kumu tana iya shekara bilyan biyar tana zama mai amfani ga rayuwa ta dan adam, tsirrai da kuma dabbobi.sun tabbatar cewa sinadari dake gewaya wa a cikinta na iska da ruwa da hasken rana, da kuma yadda wasu taurarin kewaya duniyar tana samar ma da wannan duniyar wani yanayi wanda halitta zata iya shekara biliyan biyar nan gaba ba tare da wata fargaba ba.

Amma su kuma masana yanayin sararin samaniya da iskar dake juyawa a wannan duniyar da mu ke a ciki, [CLIMITOLOGIST] sun ce akwai fargaba na tururin da hayaki wanda kere keren dad an adam keyi domin amfaninshi yana haifar da wani yanayi wanda ake barazanoni ga zaman wanan duniyar hankali kwance.wanda ya jawo hatta duk masana kimiyya sun yarda da wannan farga wadda masana yanayin kasa sukayi wannan yasa sun sama wannan hali da ake ciki da wani suna mai suna DUMAMAR YANAYI,

Shine wanda zakaji ana yawan maganarsa a majalisar dinkin duniya ana kuma kuma ta kira ga mafishugabanin duniya das u dau wani mataki na wannan yanayi da wannan duniya ta shiga na dumamar yanayi,wanda masana wannan fanni sunce duniyar na iya shiga wani yanayi wanda zata iya karewwa kwatsam saboda wasu matsaloli wanda wannan dumamar yanayi zai haifar ga wannan duniya,

Manzon Rahama Muhammad [S.A.W] Ya bayyana mana alamomin karshen duniya da yawan gaske acikin Ayoyin al kur ani mai tsarki, kuma kalamansa masu alabarka,]hadisai] wanda bincike su daki daki ya nuna fiye da kasha casa in sun bayyana,sai dai jiran lokaci kawai.Duk wani wanda ya samu wani malamin addinin musulunci na unguwarsu suka dauko hadisan da Manzon Rahama[s,a,wa] ya fada akan karshen duniya duk wani ingatatatcen hadisan da suka dauko mafi yawa zasu masa tikin din cewa ya faru ko kuma yana faruwa,ko anji labarin ya faru.wanda zakaji a wancan lokaci da Manzon Rahama[s,a.w] yayi maganar mamaki akeyi.

Masana ilmim kimiyya sun hadu akan wata matsaya da suka sanya ma suna [Grand unification theory] masanan sun amince da cewa an kai wani yanayi na bincike da ganowar kimiyya wasu masu wannan ra ayi sunce an kai karshe wasu kuma suka ce a a an dai kusa kai malejin komai.don haka sun fara ba wannan yanayi wata fassara ta karshen duniya,

Wannan yanayi wanda zaka iya fassara shi da ma anar kololuwar binciken kimiyya yasa masana kimyya na binciken me ye mafita me ye kuma makoma.ga wannan duniyar da halittar dake cikinta,?mai karatu zai yi Magana cewa shi sai kwananann ya samu wasu daga cikin fasahar kimiyya,kai kila yanazu ka samu anma can an dade ana amfani da wannan fasaha, misali fasahar yananar gizo bata fi shekara sha biyar da amfani da ita a ko ina ba,amma yanar gizo yafi shekara hamsin da ganowa da fara aiki da ita,haka wayar tafi da gidan ka,tayi shekaru kafin mu fara amfani da ita ga duniyar yaku bayi.

Yan [grand unification theory] sun aminta kawai akan cewa a binciken kimiyyay yanzu sai dai kawai a inganta wanda ake dashi amma an kai kololuwa. Sai kuma wani binciken da ganowar da ba wani amfanin da zaima mutum sai ma ya cutar dashi.sun ce bangaren likitanci ne kawai lafiyar mutum ake dad an sauran aiki wanda yanzu aka fara aikin yadda za a maida mutum sabo.[regeneration]da yin wani mutumin [cloning] binciken ya kai ga cewa suna jin zasu iya maido muryar wasu alkaryu da suka gabata,

Wani hadisin Manzo[S.A.W]Wanda na gani wani littafi [BAN SAN INGANCISA BA,BAN KUMA BINCIKI IN GANCIN NASA BA KUMA NI BA MALAMI BANE,NA KAWO ABIN DANA KARANTA NE KAWAI]

A ruwayar hadisin ance MANZON ALLAH[S,AW] An tambayi manzon Allah [s,aw] yaushene zaa yi tashin alkiyama ?Manzo[s,a,w]Yace bayan wafatinsa da shekara dubu daya da dari biyar dan wuta na wuta dan Aljanna na Aljanna ,[Allah shine masani]

Akwai wasu masana kimiyyar d azan kira da Masu miyagun makamai.su wadannan na da ra ayin cewa makaman kare dangi da ake dasu yanzu a duniya sune karshen wannan duniyar.sunyi yi wani rahoto mai suna [Nuclear arm] aciki suke cewa, makamin kare dangi ba za at taba amfani dashi ba, a wannan duniyar a yanzu,kuma kula dashi yana tsadar gaske.kuma bai da tabbas acigaba da kula dashin ba tare day a yi wani lahani ko wata illa ba,wata rana,

Wannan yasa masana kimiyya k eta binciken ya zasu yi da wandannan makaman kare dangi?ina za a dkaisu ya za a tarwatsa su a ina?in sukayi kuskuaren tashi me zai faru? Wannan damuwar na tsananin cikin kuma ana ta aikin neman mafita gay an kimiyyar kera makamai.

Wadanda makaman nan sunyi ma duniya kuri,sun sata tsakiya daya in ya tashi sai ya shafi duniya baki daya,kasasahen dake da makaman nan sune ISra ela ,Amurka ,chaina ingila faransa rasha,da wasu kasashen.masu wancan ra ayi sun ce kodai kuskuren tashin daya daga cikin makaman can ya kawo karshen duniya ko kuma wurin kokarin ya za ayi dasu su tashi kuma su tad a duniyar,sunce dole sai anyi dayan domin ko ba iya cigaba da mallakarsu da kula dasu din din dole wani abu ya faru wata rana, kuma yadda aka kera su basu iya jiimirin shekaru a ajiye ko kuma ana kula dasu, ance tsawon rayuwarsu a duniya shekara dari da hamsin ne.sai a nemi makama dasu.ko a canza ko yar.

See also  TARKON ƁERA

Daya daga cikin al ajubban wannan duniyar shine ALKUR ANI MAI TSARKI.wannan saukakken littafi daga Allah yana da ban mamaki, in ka hada shi AYOYIN DA YA ZO dasu akan wani labara kuma sai kaga anzo binciken kimiyya ya tabbatar da wannan. Shi yasa masana kimiyyya suka tabbatar da cewa AL KUR ANI KIMIYYA CE.

Wani daga ban mamakin na AL KUR ANI shine yadda Allah ya tsara komai bisa lissafin daki daki wanda masana ke sanya su sallama cewa idan ba wanda ya Hallicci halittta ba kuma yake sarrafa wannan duniyar ba wanda ya isa ya saukar da wannan TSARRARREN LITTAFIN.

Wani lissafin goma sha tara [19] wanda aka yi da AL KUR ANI MAI TSARKI Ya ba masan kimiyya da kwararrun lissafin duniya mamaki,wanda acikinsa har marigayi Ahmad Deedat ya rubuta wani littafi mai suna ALKUR ANI MU UJIZAR MU UJIZOZI.[Wanda ya sami wannan littafi zai ga wannan abin mamaki]

Da kuma yadda komai yake a tsare a lissafe daki daki,misali;

Yawan Kalmar DUNIYA 115 dai dai

Yawan Kalmar LAHIRA 115 dai dai

Yawan Kalmar mala ika 88 dai dai

Yawan KalmarShaidan 88 dai dai

 Yawan Kalmar Rayuwa 145 dai dai

Yawan Kalmar mutuwa 145 dai dai

Yawan Kalmar amfanuwa 50 dai dai

Yawan Kalmar batawa 50 dai dai

Yawan Kalmar jama a 50 dai dai

Yawan Kalmar ma aiki 50 daidai

Yawan Kalmar iblis 11 dai dai

Yawan na tsari daga gareshi 11 dai dai

Yawan Kalmar musibah 75 dai dai

Yawan Kalmar godiya75 dai dai

Yawan Kalmar sadaka 73 dai dai

Yawan Kalmar gamsuwa 73 dai dai

Yawan Kalmar batattu 17 dai dai

Yawan Kalmar matattau 17 dai dai

Yawan Kalmar musulmi 41

Yawan Kalmar jihadi 41

Yawan Kalmar dinare 41

Yawan Kalmar jin dadi 41

Yawan Kalmar sihiri 60

Yawan Kalmar fitna 60

Yawan Kalmar zakka 32

Yawan Kalmar baraka32

Yawan Kalmar zukata 49

Yawan Kalmar haske 49

Yawan Kalmar harshe 25

Yawan Kalmar wa azi 25

Yawan Kalmar tsana 8

Yawan Kalmar tsoro8

Yawan Kalmar lacca 18

Yawan Kalmar talla 18

Yawan Kalmar wahala 114

Yawan Kalmar hakuri 114

Wannan kadan kenan daga yadda komai yake lissafe kuma tsare a cikin al kur ani mai tsarki kamar yadda na dauko a wani littafi Dakta tarik ya rubuta.bashirtofa ya fassaro wani sashen littafin a littafinsa na kimiyya da al a jaban AL KUR ANI,

A irin wannan lissafin ne wani masani yarubuta wani littafin mai suna da turanci [computer speaks]ma ana kwamfyuta na Magana. Mai suna Dakta Rasheed ,inda ya yi bayanin daki daki yadda ubangiji cikin mu ujizar ALKU R ANI YA TSARA KOMAI A TSARE.a ciki yakawo yadda hatta shekarun Annabawan Allah da yadda shekarunsu yake a duniya,da tsawon yadda bambancin shekarun suke kafin wani annabi yazo.A lissafinsa kamar yadda yake a wancan littafin na [computer speaks] duniyar nan sauran shekara dari biyu da tamanin dabiyar ta ta kare[285]

Wani tsarin halitta mai ban Al ajabi daga halittun ubangiji akwai taurari,rayuwar taurari da yadda suke tafiya yana da ban al ajabi.AL KUR ANI YAZO da zancensu sosai,karatun da yadda suke rayuwa yana kara imani.t

Akwai wata tauraruwa wadda ake kira1950 wadda zan sa ma suna TAURARUWA MAI WUTSIYA.a tsarin rayuwar ta takan ratsa duniy yi ne ta wuce lokaci lokaci ta koma can wata duniyar sannan in ta dawo sai kuma ta ratsa duniyoyi.wannan tauraruwa ta wuce kuma zata dawo kamar yadda al adarta yake.

Masana wannan fanni sun ce,ba makawa idan wannan tauraruwa ta dawo tana wannan yawo sai ta bugi wannan duniyar tamu,masana sun yi sunyi suga menene mafita,har ma sun yanke hukunci cewa mafita day ace,A rungumi kaddara idan lokacin yazo masanar lokacin su nemi mafita ko kuma duk abin day a faru a lokacin a dogara gareshi.

Tabbas masana sunce 1950 zata dawo,kuma zata bugi wannan duniyar,kuma in ta bug eta zata ragargaza ita wannan duniyar domin ita karfin tauraruwar 1950 duk duniyar data doka sai ta wargazata.Anyi rubuce rubuce masu yawa akan wannan tauraruwa da halin da wannan duniyar ke ciki tsakaninta da wannan tauraruwa1950.yaushe zata zo,masana nata rubutu da bincike akai.taka mai man lokacin ba wanda ya sani,!KARSHEN DUNIYA NA HAKIKA ;ALLAH NE MASANIN GAIBU.

An tsaro wannan labarai daga littafai da rahoton kimiyya daban daban da kuma wasu littafan addinin musulunci KARSHE.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here