Majalisa Ta Gargadi ‘Yan Nijeriya Kan Amfani Da Kudin Intanet, Bitcoin

0

Majalisar dattawan Najeriyar ta nuna matukar damuwarta a kan yadda ake jan hankalin ‘yan kasar don rungumar tsarin amfani da kudin intanet na Bitcoin din, musamman a matsayin wata hanyar zuba jari da ke rubbanya riba cikin sauri.

Majalisar ta nuna damuwar ne bayan wata muhara a ranar Talata a kan wani kudurin da wani dan majalisar, Sanata Benjamin Uwajumogu ya gabatar.

Majalisar ta ce tana sane da cewa jaridar The guardian ta Amurka ta taba wallafa cewa, babban bankin zuba jarin nan na duniya, JP Morgan, ya bayyana cewa kudin gizon ya fi dacewa da masu safarar miyagun kwayoyi kuma ba zai kai labari ba.

See also  'Yan sanda sun kaddamar da farautar kame masu sayar da sabbin takardun kudi na Naira

Haka kuma babban bankin kasar wato CBN bai amince da amfani da kudin na Bitcoin a hukumance ba, duk kuwa da cewa bankin da kasuwar shunku ta kasa da kuma hukumar inshora na kasa ba su yi wani hobbasa ba na wayar da kan jama’a a kan hadduran da ke tattare da kudin gizon.

Daga BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here