Cutar Kwakwalwa Da Yadda Ake Tafiyar Da Ita

0
Daga Sulaiman Bala Idris
Mutane da dama suna fama da cutar kwakwalwa, don haka ne ma masana kimiyyar zamantakewa da sanin halayyar jama’a suke dan shan wahala wurin gudanar da bincike dangane da wannan maudu’in. Akwai wasu daga cikin masana wadanda suka tafi akan cewa ta cutar tabin hankali shifci ce. Saboda a nasu takaddamar, cutar kwakwalwa na iya zama dabi’ar me ita har ta girmama zuwa tabin hankali, wanda kuma al’umma suke kallo a matsayin nakasu, da abin ki da kyama.
A sakamakon haka, duk wanda aka cewa mai cutar kwakwalwa zai zama abin ya yi mishi ciwo, ko da kuwa ya na da wannan matsalar, amma a hankali al’umma zasu gamsar da kwakwalwarsu cewa da gaske su masu tabin hankali ne, don haka sai jama’a su ci gaba da mu’amala dasu a matsayin tababbu. Bayan tsawon lokaci an samu wasu masanan da suka yi martani ga wannan tunanin da ke cewa cutar kwakwalwa shifcin gizo ce. Masu wannan martanin sun tafi akan cewa cutar kwakwalwa wata aba ce tabbatacciya kuma wacce tarihi da rayuwar al’umma suka tabbatar da samuwarta.
A na iya fahimtar cutar ta siffofi daban-daban, saboda tana da alaka da yanayin jikin mutum, tunani, muhallin da yake rayuwa, da kuma irin al’ummar da yake a ciki. Masana a fannin kwakwalwa sun yi kokari sosai wurin bambancewa tsakanin cutar tabin hankali da cutar kwakwalwa. Tabin hankali na hana mutum ya gudanar da al’amuran yau da kullum na rayuwa, ko da kuwa zai gudanar, ba zai iya yin komi cikin tsari kamar yadda kowa ke yi ba. a daya bangaren kuma cutar kwakwalwar c eke girmama ta zama tabin hankali, saboda ita cutar kwakwalwa ba kowanne mataki bane a ke kai mai ita asibiti, sannan ba a kowanne mataki bane mai ita ke shan magunguna, wani ma bai san yana da it aba, amma a dabi’unsa da zaran masana sun gani, zasu iya fahimtar cewa yana da ita.
Daga cikin cututtukan kwakwalwan da ke gawurta su zama tabin hankali akwai barazanar ‘Shizoprenia’ da ‘Maniac-Depression’ da dai sauransu. Daga cikin mafi shaharan nazari akan cutar kwakwalwa da tabin hankali, shi ne aikin mashahurin masanin nan mai suna Michel Foucault, a littafinsa mai suna ‘Madness and Cibilization’, wanda a ciki ne ya kawo jadawalin tarihin tabin hakali daga shekara ta 1500 zuwa shekara ta 1800, domin kawai ya iya fahimtar yadda fahimtar lamarin tabin hankali ya samu sauyi a tsawon lokaci. A ta bakin Foucault, kafin wannan zamanin namu, rashin hankali, da cutar kwakwalwa wani abu ne da ba a dauke shi a matsayin komi ba, bilhasali ma ba a kange su daga yini rayuwar yau da gobe da su, kamar yadda ake yi a yau.
Masu cutar kwakwalwa da tabin hankali na iya yawo a kan titi ba tare da an samu yara na yi musu wakokin mahaukata ba, ko su rika bi suna jifansu ba, sannan ba su sa yagalgalallun kaya. Sai a bayan karnoni na 17, da 18, da 19 ne aka fara yiwa masu cutar kwakwalwa da tabin hankali a matsayin barazana ga al’umma. Sannan ne lokacin da aka fara tsangwamarsu, aka fara yi musu wakokin mahaukata, da tsokana iri-iri. Haka nan kuma a wancan lokacin ne aka giggina gidajen mahaukata, inda aka bambance tsakanin masu tabin hankali da sauran al’umma. Sannan masani Foucault ya bayyana cewa mutane na kallon tabin hankali a matsayin wani abu wanda ya shafi wasu kaskantattun da basu da ‘yanci. Sai yace, ya kamata a fahimci cewa cutar tabin hankali tamkar yarinta ne, kamar yadda iyaye suke tarairaiyar ‘ya ‘yansu tun daga matakin jariri zuwa balaga, don kawai ‘ya ‘yan su siffantu da siffofin mutanen kirkiki; haka ma masu tabin hankali suke bukatar a tarairaiye su, a basu kulawar da za ta iya sauya cutarsu daga hauka zuwa hankali.
Kamar yadda ake horas da yaro idan yayi laifi don a nuna mishi cewa kuskure ne ya aikata, haka ma mai tabin hankali ko ciwon kwakwalwa na bukatar idan ya yi kuskure a nunasshe shi ko da kuwa da horo ne. sannan idan yaro yayi kwazo ko hazaka ana bashi tukuici, haka ma mai tabin hankali idan ya yi wata bajinta ko abin da ya dace da hankali, sai a yi mishi kyauta ko tukuicin da zai say a rika tunawa. Tarihi ya adana cewa a farko-farkon karni na 21, an samu matsalar rashin bayar da kulawa ga da yawan masu tabin hankali, sai ya zama ana banzantar da su ne. akai wadanda sun samu tabin hankali ne sakamakon shaye-shayen miyagun kwayoyi, barasa da sauransu, wanda kuma a wancan lokacin su ne manya-manyan dalilan tabin hankali a farkon wannan karni. Alkalumma sun nuna cewa maza da ke shekaru 18 zuwa 44 ne ke fama da wannan cutar ta tabin hankali. Su kuma mata sun yi ta kamuwa ne da cutar bayan sun haihu. Wata a asalinta bata da cutar, amma da zaran bayan ta haihu, sai ta kamu, wannan kuma ya na afkuwa ne sakamakon rashin bibiya da zuwa wurin likita. Ya kamata idan mace ta haihu a je wurin likita duba don ya tabbatar da lafiyarta. Haka kuma a farko hanyoyin dakile cutar kwakwalwa da tabin hankali guda ne, shi ne a kai mutum asibitin mahaukata, ko na masu lura da masu cutar kwakwalwa, inda ake basu magunguna bisa tsarin likita, a can din ma wuraren ajiyansu daban-daban ne, cutar ta wasu ta fi ta wasu gawurta.
Wannan kebe masu tabin hankalin da ake yi, da kuma magungunan da suke sha, ya na basu damar su iya fahimtar cewa lallai da gaske suna da matsalar kwakwalwa. Amma daga baya sai aka samu ci gaba, ta yadda da zaran an kawo mutum mai cutar kwakwalwa, matukar cutar ba ta gawurta ba, sai a bashi magani kawai a sallame shi ya koma gida. Zaman mai cutar kwakwalwan a cikin al’umma, matukar zasu kiyaye ka’idaji da sharuddan da likita ko masanin kwakwalwa zai gindaya musu, zai warware a dan wasu lokuta. Abin da ya aka fara sallamar masu cutar kwakwalwar da cutarsu ba ta gawurta ba, shi ne don a kauce ma takura musu. Saboda da yawa masu cutar kwakwalwar cutar tasu ba ta yi kamarin da za a je a killace su ba. a dalilin haka, idan aka yi kuskuren killace su daga al’umman kuma, hakan zai kara girmama matsalar tasu ce maimakon a magance ta, wadannan wasu abubuwa ne da ba dole likita a asibitin ‘Psychiatry’ ya fahimta ba, saboda shi an bashi horo ne akan yadda zai magance cutar kwakwalwa da kuma irin magungunan da mai cuta zai sha a matakin cutar tashi.
Amma bai yi karatun sanin halayyar mai cutan ba, da kuma irin hatsarin da ke cikin killace wanda cutar tasa ba ta yi kamari ba, wannan kuwa aiki ne na masana kimiyyar zamantakewa da sanin halayyar dan adam. Wasu cutar kwakwalwarsu ‘yar karama ce, abin da suke bukata shi ne a rika zuwa da su wurin likita ko asibiti domin su yi mishi bayani ya basu magani. Irin wadannan su kuma akwai hatsarin gaske a ce za a kwantar da su a asibitin mahaukata ko masu cutar kwakwalwa, saboda su fa basu gama gamsuwa dari bisa dari cewa cutar kwakwalwa c eke addabarsu ba, idan kuma aka kwantar da su a irin wadancan asibitoci, zasu sanyawa kansu damuwar cewa makusantansu da al’umma na yi musu kallon masu tabin hankali ne; daga karamar cuta za a baro babba. Allah ya kara tsarewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here