Musulunci da musulmai su suka kawo duk wani cigaba a komai na duniya,kowane fanni ka fara bincikensa na tarihin kawo shi. Da kuma cigabansa a duniya zaka ga cewa Musulmai sun taka wata irin rawa wadda ba wanda ya taka kamarta a duniya.
Zaka ga nasu sunyi shi cikin tsafta da ilmi da kuma basira da hikima amma aka dauki nasu aka gyara ko aka yi ma illa koma aka bata shi ko kuma aka ingantashi aka maida shi hankaka maida dan wani naka.ma ana wadanda suka sata daga musulunci su yi karyar cewasune ahlin abin.
Duk wani cigaban duniya ya samo asali ne daga adabi,watau rubuta littafi, wanda ,marubuta kanyi don su fito da wani ilmi ko suyi wani hannunka maisanda ko kuma suyi wata nusarwa.Rubutu ne farko sai a maida shi wani tabbatacen aikin ilmi.
Daya daga cikin littafin da Abu da uwargidansa suka aiko mani daga Landan akwai littafin nan Mai suna DARE DUBU DA DAYA.fassarar turanci wanda keda sifili uku. Kowane sifili yana da shafi dari tara da Hamsin.950.KUma rubutun kana na ne. so sai.
Wannan littafin shine wanda ba littafin dab a taba kamarsa ba a tarihin adabin hikaya.a duniya.shine littafin da yai tasiri gaduk marubutan hikaya na duniya kuma har yanzu ana kwafa daga gareshi har yanzu ba kureshi ba.Anyi fina finai dayawa daga labaran littafin.
Ba wani yare Babba a duniya da ba fassara wani bangare na littafin a Harshen yaren ba.ko kuma aka kwaikwayi salon littafin aka yi wani littafin da wannan yaren.Misali salon da kuma labaran littafin aka dauka aka rubuta littafin MAGANA JARI CE TA DAYA ZUWA TA UKU.wadda marigayi Abubakar imam ya rubuta.
Haka kuma tun zamanin turawa an fara fassara littafin da Hausa, wanda wani bature ya fara har rubutun ya kai dare n a dari da hamsin sai ya tsaya. Kamfanin Gaskiya co orparation dake zaria.ya yi aikin buga littafin sai dai shi a littafin farko dan biyu, Hausar bata karantuwa. Sai daga littafi na uku ne, littafin ya fara zaka iya karantwa ka gane sunansa DARE DUBU DA DAYA. An buga shi daga littafi na daya zuwa na biyar aka tsaya.Ana samunsa Har yanzu a kasuwa,
Rubutun bana yi shi bane a matsayin wata takardar d azan gabatar don,ilmim adabi. Dana kawo marubutan kasashe da suka shahara a kasashensu amma bisa dogara da kwaikwayon da kuma dauko labarai daga littafin Dare dubu daya suna sarrafa shi.A kasashen asiya turai da amurka.gabas ta tsakiya da kuma afrika.
Farfesa Ibrahim Malumfashi malami a jami ar usman dan fodiyo dake sokoto.shine shaihin malamin daya goge akan sanin tarihin wannnan littafin da kuma yadda aka rubuta shi.Malamin masani ne so sai akan salon adabin wannan littafin da kuma tasirinshi a duniya.ya rubuta takardu na ilmin adabi masu yawa akan wannan. Ya kuma yi littafi. Akan Rubutu da rayuwar Abubakar imam. Wanda a cikin ya kawo yadda littafin Dare dubu da daya yayi ma imam tasiri,da kuma tasiri ga rubuce rubucensa.
Dare dubu da daya shine tasirin da yayi ma kasar Hausa da kuma AFrikawa wanda ta jawo aka san kasar da yin tatsuniya da dare. Wanda ada uwaye kanyi ma ya ya don a hana su fita suje yawo a waje ko kuma a tsuniyar a kawo wasu hikima mai tasiri wanda zata kawo ma yaro wani darasin rayuwa.
Wani abu da littafin dare da daya shine ba wanda yasan waya rubuta shi.ko kuma suwa suka rubuta shi.wani abu ne wanda har yanzu ake muhawarashi a duniyar adabi da kuma ilmin tarihin littafin.wasu sunce mutum daya ne da iyalashi su kayi aikin wasu suka ce a a agungun mutane suka yi aikin,
Hatta tsawo lokacin da aka dauka ana aikin littafin ana muhawara akanshi.wasu sunce lokaci guda akayi aikin wasu kuma sunce a a tsawon lokaci aka dauka wasu sukayi suka tsaya a wani wuri wasu kuma suka dasa da haka aka samu littafin.
Amma abin da aka samu tabbaci akayi duk wanda ko wadanda suka rubuta littafin malamai ne masana addinin musulunci.domin yadda a littafin ake gwada tsananin fahimta na addinin musulunci.wasu kuma suna da muhawarar cewa wanda yayi rubutun wani sufi ko kuma sufaye ne. saboda yadda ake yawan nuna girman Allah acikin littafin.An fara littafin ne da basmala.da salati
Akwai ma masu muhawarar cewa marubutan ko marubucin dan a kidar shi a ne.saboda yadda a rubutun littafin ake tona yadda sarakuna dake rayuwa wancan lokacin ke rayuwa. Kuma suna kiran kansu sarakunan musulunci.irin tabargazar da suke da kuma aika aika.wannnan yasa masu wannan ra ayi sukace marubutan shi a ne don su nunama yana baya abin day a faru a wani salon rubutun koda kuwa an danne bullar littafan tarihi.da kuma yadda a duk labaran dake cikin littafin zaka ga akwai girmama sunaye irinsu Fatima. Hassan, Husaini da sauran sunaye wadanda malaman shi a ke girmamawa.
Ana tsammanin an rubuta littafin ne. a zamanin mulkin sarkin dake kira na musulunci Haruna Rashid.wasu kuma sun ce bayan shi. Wasu kuma sunce an fara rubuta shit un zamanin Haruna Rashid, rubutun ya dau tsawon lokaci har zuwa wajen sarakunan MUsulncin zamanin guda hudu ko biyar.wannan yasa ake ganin tabbacin cewa rubutun gadonshi aka rika yi.wasu ko wani yatsaya a wani wuri wasu kuma suka dasa Su ka cigaba , tayiyu kamar yadda akayi masu wasiyya.
Asalin littafin an rubuta shi ne da larabci da sunan ALFUN LAILA WA LAILA.Ma ana dare dubu da daya. Faefesa Malumfashi. Ya rubuta a littafinsa dabin Abubakar Imam. Cewa akwai muhawarar cewa asalin littafin na Alfun Laila wa laila.da farisanci aka rubuta shi fassarashi akayi zuw larabci. Na larabcin ne ya shahara. Ya danne. Na farisanci.harma ya badda shi a tarihi.
Bugun tarihin larabci da ake dashi.an nuna an fassaro shi ne daga wani yare.wanda yana yi labaran dake ciki aka gane daga farinsanci ne.da kuma irm wakokin da marubucin ya rika kawowa.ittafin bugun farko yana da sifili goma sha biyu.amma an rika tace shi don ya zama karami dai dai samuwar kowa har akayi wani sifili biyar waani uku,
Littafin ya cika duk wata kaida ta adabi. Salon labari .dadin labari wasa da harshe da kuma hasashe da hannunka mai sanda da ban tsoro da wa azi ban tausayi ban takaici. Da jin haushi.waka was an kwaikwayo. Da kuma rike mai karatu yaji in ya fara sai ya kamala.har yanzu ba ai littafin tatsuniya da aka zuba hikima kamarsa ba.kuma babu wata Nahiya a duniya da mai littafin bai tabo ba awani yanayin laarinsa.
Wani lokaci kuma akan rika rairaye labara nana littafai dasu aba littafan suna daban daban ana rubuta cewa ana dauko ne daga littafin dare dubu da daya.da haka littafin da labaransa ya watsu ba tare wani ya taba gani hakikanin littafin ba.
Fassarar turanci ta littafin kamar yadda farfesa Malumfashi ya shaida mani. Akwai mai sifili goma sha biyu shima.karamin shine mai sifili biyu, wanda an tace an kuma tsamo muhimman labaran acikin sifili biyu. Kawai, Amma a turanci anyi dinbim littafai da labaran littafin.
A india da kasar chaina nan ne akayi ma littafin wani irin fassara domin sunce wasu labaran littafin sunyi kama da al adunsu na hindu da buddah nan ne suke da cikakken fassarar littafin mai sifili ar ba in,da dimbin littafai da fina fina daga littafin.Farfesa Malumfashi yace mani a tarihin duniyar adabi ba wani littafin da yayi tasiri a duniya kamar dare dubu da daya.littafin ya taimaka wajen bincike da fahimtar musulunci, a yankin, harda wasu wuraren,na asiya da turai.
Don ba yadda zaka karanta littafin ka tsallake koyarwa musulunci da sakonsa.saboda a rubutun an girmamama sakon da musulunci yazo dashi.wannan yasa wani manazarcin littafin wanda ba musulmi bay a rubuta cewa yana da wuya ga wanda ba musulmi ba. Ya gama nazarin littafin. Bai koma yayi nazarin addinin musulunci ba.
Littafin ya ginu ne bisa labarai na almara da ta tsuniyi masu hikima da koyar da darasi da kuma jan hankali da dadin gaske.wasu kuma misalan labarai ne da suka faru a tarihin zamanin jahiliyyar larabawa wasu kuma zamanin bayyana da kuma bunkasar musulunci.
An karkare da cewa wanda ya fara ko suka fara rubuta littafin sun fara bisa wani bacin rai ne. saboda salon yadda suka faro rubutun dashi
Asalin labarin ya fara ne daga wani sarki mai suna shahr yar wanda ke mulkin wata Babba kasa wata rana dan uwansa wanda shima sarki ne. a wata kasar sarkin mai suna shahzaman.ya aiko masa yaje yana son ganinsa.ya yi ban kwana da fadarsa da matansa da barori ya kama hanya.har ya yi nisa sai ya tuna da yayi mantuwa,ya dawo a sukwane don ya dau abin day a manta a fadarsa.yana isa sai ya ike matarsa da wani bawansa. A bisa gadonsa, nan ya kasha su.
Ya isa wajen wancan sarki cikin Bakin cikin abin da ya gani.ya shiga wata irin damuwa. Wadda ko ina bai iya fita a fadar inda yazo bakunta. Wata rana yana zaune a dakin bakin da aka aje shi shi shi kuma mai masaukin bakinsshi ya tafi kilisa. Sai ga matarsa da wani mutum bawan sarkin sun fito suna watayawarsu.
Wannan yasa zucizyzrsa tace ashe wannan cin amana ba wai a gidansa kawai ta kare ba.don haka sarki shahzaman na dawowa sai ya bashi labarin abinda ya gani a gidansa da kuma wanda shima ya gano gidansa day a baro.
Sarki shahzman na dawowa daga kilisa. Abokinsa sarki shahryan ya kwashe labarin abin day a gani ya faru gidansa ya fada masa. Ya kuma bashi labarin abin da ya same shi a gidansa.da bakin cikin dake damunsa tun day a zo.suka tsara yadda sarkin zai boye a dakinshi ya yi kamar ya tafi kilisa domin ya gane ma idonsa dil.
Haka suka yi suna boye a inda suke sai ga matar sarkin nan da wani bawan gidan sun fito sune sheke ayarsu, wannan abu ya sasu cikin wani bakin ciki. Suka shirya fita garin su shiga uwa duniya har sai sunga wani abin takaicin day a fi nasu.
Bayan sun bar fada suka dosa tafiya a dokar daji.sai suka zo wani waje da dare yayi masu. Suka daure dawakansu. Suka hau saman kololuwar itace don su huta kafin safe suci gaba da tafiya.can tsakar dare sai ga wani aljani ya dawo daga tafiya shima ya sauka kasan itace domin ya huta.bayan ya zauna sai ya dauko wani akwati ya fito da wata yarinya kyakykawa. Yace mata kema fito ki motsa jininki kafin in danyi barci.
Yarinyar ta fito ta gyara gashin tat a kuma dauko jita tana kadawa har Aljanin na yayi barci. San nan ta farad an yawo tana motsa kafarta.daga kanta da za tayi sama. Sai ta Hangi wadan nan sarakuna biyu. Nan take tace ku sauko. Suka fara gardama tace koo ku sauko ko in tayar da wannan aljani daga barci ya halaka ku.
Daga nan sai suka sauko . suna saukowa tace kowa cikinsu sai yayi amfani da ita.ko kuma ta tayada aljanin nan ya kasha su.nan su kayi bayan sun yi tace kowa ya bata zobensa suka bata. Ta dauko wata jaka ta hada da wasu zoben dake aciki.tace kune na saba in da kuka yi amfani da ni ina ahannun wannan aljanin.
Ta basu labarin kanta da cewa ita diyar sarki ce. A ranar daurin aurenta wannan aljani ya sato ta.kuma yake yawo da ita don kishi don karma wani da namij ya aganta.tace amma tana wajenshi ta sadu da maza sarakuna saba in. har dasu.tace masu kusan in diya mace na son abu duk duniya ba wanda ya isa ya hana ta samunabin da take so.
Wannan labarin ya sa sarakunan nan suka dawo gida. Sun ji wani abin da yfi nasu ban al ajabi.sarki shahzaman ya zuwa ya aka kasha matarsa da bawan da suke holewa tare.ya kuma ce bai karaaure. Amma duk Dare yana son a samo masa budurwa wadda zai kwana da ita da safe ya kasha ta.
Haka ya rika yi tsawon zamani har yan matan garin suka kare wasu kuma suka gudu.suka koma wasu garuruwan.ya rage gidan waziri kawai yake da wasu yan mata guda biyu Babbar sunanta shaharzad karamar sunanta dunyazad.duk kaninsu waziri yasa masana sun karantarsu da ilmi so sai. Kuma shaharzad ta rika gwamuza da baki in sunzo gidansu tanajin labaran fatake da kasashe.
Wata rana waziri ya dawo gidansa ransa bace.ya yansa suka tambaye shi lafiya? Ya fada masu cewa gobe babu budurwar da zai kaima sarki. Don duk garin bay an mata kodai ya kasha su ko kuma sun gudu.yaje kasuwar bayi babu, an bar kawo wa tun da an san me ake dasu a garin.kuma sarki sawa zai yi a akshe ni in ban cika maganarsa ba zuwa gobe.
Sai babbar diyarsa tace Baba gobe ni za a kai.shahazad ta gamsar da babanta gobe a akaita. Nan suka zauna da jimamin daga gobe ba akara ganin diyarsu.ta kuma kara dacewa gobe in zan tafi zani tafi ne da kanwata dunyazad.nan ma waziri ya shiga wani taskun nab akin ciki.Shahazad ta shirya da kanwarta cewa gobe in munje .bayan mun gama abin da zamuyi da sarkii ki roke ni cewa in dan baku labari kafin safiya tayi.ni kuma zan fara
Wanshekare sarki da diyar waziri suna fada suna jiran safiya tayi a tafi da ita akashe.kamar yadda a ke yi.sai Dunziyad tace yar uwata kafin safiya ta ida hauni yazo yagama aiki akanki ko zaki bamu wani dan labari daga labaran da kikia sani ?shaharzad sai ta fara.kafin ta kai karshe sai rana tafito.
Sarki sai cewa yayi bani kasha ki. Sai gobe kin gama wannan labarin.Daga nan ne labarin DARE DUBU DA DAYA YAFARA.Ta rika saka labari cikin labari.wata irin hikima mai ban mamaki.ta kuma rika kawo waka da kalaman batsa. Don ta daga hankalin sarkin ya kara rike ta.
Da wannnnan labarin na duk dare ta sanya sarkin yayi nadamar abin day a aikata abaya.kuma ya canza tunaninshi na mummunar kallon da yekama mata. Kuma ya shin fida adalci a kasar sad a yankinsa baki daya .ya kuma aure ta.labarin yak are a dare dubu da daya bayan a wata ruwayar sarkin ya mutu. A wata kuma ya auri shaharyazad..Dare dubu da daya shine littafin da ba ai kamarsa ba adabin duniya.kuma ba ba a san waya rubuta shi ba.