Kamfanin Layin MTN: Gawurtattun Barayin Zaune

0

Daga ISB Daurawa

Wadanda su ka san wayar salulata, za su shaidi yadda lambar da ake latsawa a kira ko a kasha kira (green & red button) su ka kode, su ka wahala kamar wanda aka shekara bakwai ana aiki da su. Duk kuwa da cewa wayar ba ta wuce wata guda ina aiki da ita ba.

Akwai wata shahararriyar jaruma wacce duk wayar da za ka gani a hannunta sai lambobin kashewa da amsa kira (dial and reject) sun kode ko da kuwa sabuwar waya ce. Watarana ina zolayarta na ce wai duk amsa waya ne ke jawo wannan?. Ta ce a’a, yawan yin amfani da turare ne da take yi ya tsofar da wadannan lambobi.

Ni dai na wayata ba wani turare, bilhasali ma bana amfani da turaren da zai iya taba hannuna, da wani turare mai suna ‘Bod men’ na ke aiki, kuma shi feshi ake yiwa jiki da shi ba shafawa a hannu ba. Toh me ya tsofar da lambobin kira da kashe wayana?. Na san tambayar da za ku yi kenan.

Gurbacewa da lalacewar yanayin netawok ‘network’ din kamfanin layin wayar salula na MTN ne ya jawo min wannan kodewa da tsofewar wasu lambobin waya. Wanda kuma bana tsammanin ni kadai na ke fuskantan wannan matsala, duk wani mutum mai yawan amsa kira da kiran waya, zai iya samun makamanciyar matsalan.

Wahalhalu da matsalolin da layin MTN ya ke ba ‘yan nijeriya, idan da wata qasar da mutanen kirki ke mulki ne, da tuntuni an fatattake su, an kuma qwace wasu qadarorinsu saboda asarorin da su ka jawowa ‘yan qasa.

Wani abun ban haushi da wannan layin wayar na MTN shine yadda su ke tamkar wuta ba su qoshi, kullum samun maqudan kudade su ke yi da ‘yan Nijeriya, amma kuma sa ke neman hanyoyin musgunawa da cutar da masu amfani da layinsu su ke yi.

Shi dan fashi hanya yake tarewa da jibgegeyar bindiga, ko kuma ya haura gidan mutane da tsakar dare su na barci, ya nuna masu bindiga, su bashi kudi ko ya yi harbi. Amma su MTN, ba ruwansu da bindiga, matuqar kana aiki da su, sai dai idan ba su ga daman kwashe maka kudi a asusun ajiyan kudinka ba.

Duk wanda ke aiki da layin MTN ya san cewa a ‘yan kwanakin nan an yi fama da matsalar idan ka sa kudi, sai ka duba, ka ga sun debe wani kaso a ciki.

Layukan waya 3 ne su ka fara mamaye Nijeriya, layin MTN wanda ya ke qarqashin wani kamfani na ‘yan Afrika ta Kudu (South Africa), da layin ECONET wanda ya ke qarqashin wani kamfani na Zimbabiwe (a wancan lokacin kafin a sayar da shi), sai kuma layin MTEL wanda ya ke qarqashin kamfanin Nitel. Layin Mtel shine mai sauqin kudi da farko.

Duk fa da wahalar siyan layi da tsadar da ya ke tattare da shi, ba wai yana nufin idan ka siya layin komi dai dai ba kenan. Wani sabon ciwon kai shine amfani da shi bayan ka samu nasarar hada waya.

Da farko layukan sadarwar sun yi ta samun matsaloli wanda su ka ta’azzara, kawai a wancan lokaci mutane ba su mayar da hankalinsu ga nuna damuwa sosai ga matsalolin bane saboda ana doki da murnar shigowar GSM Nijeriya, kuma ba wani abu bane da ya yawaita a gari.

Cikin matsalolin da mai wayar GSM ka iya fuskanta a wancan lokaci sun hada da wahala wurin loda kudi (recharging account), da kuma shan wahala sosai kafin ka iya samun lamba idan za ka yi kira. Sannan kuma akwai matsalar idan ka loda kudi a layinka, haka nan sai ka duba ka ga an cire wani abu ko a cire duka ma, sannan kuma akwai adadin kwanakin da kudi ke yi a wayar ya lalace.

See also  Abubuwan ban mamaki goma dangane da zuciya.

Abun da wadannan kamfanonin layukan waya su ka yi a Nijeriya shine ainihin abun da ake kira cin kare ba babbaka. A dake ka a hana ka kuka.

Wani babban abun baqin ciki da kamfanin MTN su ke yi, wanda ba don sun raina wayon ‘yan Nijeriya ba, ba za su taba aikata haka ba, shine yadda kullum su ke bullo da sababbin caca, wanda za sub uqaci mutum ya yi rijista akan kudI naira 100 ko 200, domin samun damar shiga wannan gasa.

Idan da ace anan kawai wadannan ‘yan fasa qauri (MTN) su ka tsaya, da sai a ce da sauqi, amma bayan haka sai kuma netawok ‘network’ din na su ya zama kullum akwai matsalar da ya ke haifarwa.

A can baya akwai lokacin da aka yi yayin layin na MTN baya yiwuwa ka yi kira ko a kira a Kaduna, da zaran duhu ya fara shigowa, bayan magriba. Wannan matsala sai da aka dauki lokaci mai tsawo ana fama da ita. Kuma mutane da dama sun yi asara a kasuwancinsu da sauran al’amuran rayuwa.

A ‘yan kwanakin nan layin na MTN ya gurbace iya gurbacewa, ya haifarwa jama’a da matsaloli da daman gaske. A lokacin da kamfanin ya lura an fara babbala layinshi, ana kuma jifa da su, sai su ka munafunci jama’a da wani shiri na musamman, wanda su ka yiwa take da ‘Magic number’.

Shi salon ‘magic number’ abu ne wanda kowanne mai aiki da waya zai so. Domin kuma idan mata ka ke da ita, za ka sa lambarta ku yi rijista a cire ma Naira 200 a wata, sai ku yi ta kiran waya kyauta.

Wani abokina ne ya fara bani labarin wannan garabasa na ‘magic number’, bayan da na ga yayi wayar awa 1 da wani abu. Sai ya amshi wayata ya shigar da ni. Ni ko da aka sa ni a sahun ‘magic number’, na yi imanin watan watarana MTN za su bata ran masoya, su ruguza wannan tsari, domin ba taimako su ka zo yi Nijeriya ba, yaudara da dabara su ka zo yi.

Haka kuwa aka yi, kawai sai kamfanin na MTN su ka janye wannan garabasa na ‘magic number’, bayan da kusan dukkan mutane su ka saki jiki, wadanda ma basu da layin MTN da yawa sai da su ka siya.

Mutane sun tsinewa kamfanin MTN iya tsinewa, saboda dakatar da wannan garabasa da su ka yi, kuma abun haushin shine sun ka sa fitowa fili su bayyanawa jama’a cewa sun daina wannan abu, sai dai ma qara yaudarar mutane da suke yi na cewa garabasar za ta dawo wani gyara su ke yi a saurare su.

A ‘yan kwanakin nan, babbar matsalar da MTN ta bulla da shi kuma shine idan ka nemi mutum a waya, ko a kunne wayar ta ke ko a kashe sai su ce ma ka wayar a kashe ta ke. Haka nan idan ka siya katin waya za ka loda, sai ka yi ta samun matsala.

Matsalolin MTN ba su iya lissafuwa a shafin jarida, sai dai a babban littafi mai mujalladai, domin kuwa sun mayar da ‘yan Nijeriya saniyar tatsa. Su na hada baki da mahukunta, su na yin abun da su ka ga dama.

Amma ai akwai ranar qin dillanci, ranar da mutanen da ke aiki da layin MTN za su yi zuciya, su wancakalar da qwallon mangoro, sai mu ga tsiya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here