A Tsawon lokaci da wannan mujalla ta dauka tana bincike ta gano Alhaji Abdurahaman Bashir musa shugaban kamfanin Rahamaniya shine Matashi day a fi kudi a Najeriya,Mun tabbatar da haka ne bisa la akari da shekarunsa da kuma yadda ya sami kudinsa bata hanyar gado ko siyasa ko kuma kwangilar daga wata gwamnati ba. Yadda ya fara daga karamar sana a ta bisa tebur da har ya zama hamshakin Attajirin da yake gogawa da mutane irinsu Dangote.
Amma karancin shekaru da kuma raunin ilmin addini da na boko da miyagun abokai yan fada suka jefa shi cikin rikicin da har yanzu ayake ta jaeka kadawo a kai,kuma ayke bukatar addu a kafin ya samu ya fita daga wannan kakaniya.
Bincike ya nuna Alhaji Abdurahaman yanzu yana da shekara talatin da biyu a duniya,Dan asalin cikin birnin sokoto ne, Mahaifinsa alkali ne a kotun shara a, duk karatunsa ana firamare da sakandire a sokoto yayi wanda yana gamawa ya shiga gaba da sakandare domin karatun diploma abin daya kasa. Aka koreshi domin ya kasa cin jarabawa
Abokansa a sokoto sunce mutum ne wanda tun yana yaro yana fadin cewa shi f miloniya ne wanda tun ya na makaranta yakan saida alawa taba da biskit ga abokansa, wanda daga baya ya kafa tebur a akofar gidansu yan sana ar tureda,da abu yai karfi ya samu bashin kiwos wanda yake biya a hankali ya kafa yana dai sana art a tureda,kama har ya koma a cikin sokota yake yawatawa a sana arsa.
Bai taba zuwa ko ina bas a sokoto da kewaye. Abokansa sun fada mana cewa .labarin da yake ji na kano tumbin giya cewa ko da me kazoo an fi ka, yasa yayi niyyar zuwa kano ya ganta kuma yai kasuwanci.musamman da yaji ana fadin cewa a kano mai sana a sai yayi kudin gaske,wata safiya kawai sai yayi sammako ya nufi kano neman sa a.Bai san kowa sai wadanda aka hada shi dasu su taimake shi. Yayi sana oi a kano kafin ya fada.kafin ya hadu da wani mai harkar Wanda ake kira da A A RANO. Rano ya dauke shi aikin harkar mai wanda har ya aki matsayin yana tura shi fatakwal da legas ya samo masa mai.
Bashir yana da wayo da hikimar da komai rumtsi zai iya samo mai wanda wannan yasa kullum kudi masu yawa ke wajensa domin kawai ya biya ya kuma samo mai ya lodo su zuwa arewa, wadanda suka shi sunce mutum ne mai kyauta wanda abin hannunshi bai rufe masa idoba,kuma yana da gaskia wanda in ka bashi aiki sai kamala maka aikin ka cikin nasara sannan yake fitar da ribarsa,yana kuma da hazaka da kumaji .ba rago bane ko kadan
Da basher yai karfi ne a legas. Sai ya zamana ba kudin AA RANO kawai yakekula dasu ba a samo amai daga arewa kusan kudin duk wani dan Arewa maia harkar mai da basher yake takama. Wajen ya zai samo mai, wannan ya sa kullum bankuna suna da kudin dake jira an turo mashi wanda sun kai biliyoyi.wannnan matsayi ya kais hi duk wani mai harkar shigar da mai a kasar nan abokin Bashir ne irinsu Femi otedola daya daga cikin wadanda aka ce sunfi kudi a duinya. su Dangote su jimo Ibrahim duk a tebur daya suke cin abinci.
Y a sami kafa kammfaninsa ne mai suna RAHAMANIYYA da kuma iznin shigo da mai.bayan da bankuna suka matsa mashi cewa ya kamata ya fsrsc in gashin kanasa .su kuma su bashu duk kudin da yake bukata mai makon zama dan kamashon manyan attajirai na Arewa masu harkar mai.wanda bayan rijistar kamfaninsa,sai kuma lasi day a samu n shigo man.halinsa na gasakiya a sana a yasa ko wane banki yana ruge ruge a yi huldar kasuwanci dashi.
Kamfaninsa ya zama yana da tankoki sama da dari bakwai da gidajen mai sama da guda dari da hamsin da shidda duk a fadin kasar nan, da jiragen dakkon shigo da mai har guda bakwai wanda kowane kudinsa ya kai dala miliyan tara, yana da wurin tara mai wanda shine mafi girma a kasar nan wanda kudinsa ya kai biliyoyi,.kudin shigar day a kan samu daga har kai mai ya kai naira miliyan dari shidda duk watan Allah ta ala.
Daga baya a ya fadada aiyukan kamfanin nasa zuwa wajaen bangaren gine gine da kasuwancin kasa da kasa, da gidaje da safiyo, da kuma jari a mayan kamfanoni masu fada aji a kasar. Kamfaninsa yana da sama da ma aikata dubu goma a fadin kasar nan, ku ma mafi karancim Albashi a kamfaninsa shine wanda ke daukar Albashin naira dubu Hamsin a wata,
A SOkoto sunan Bashir suna ne dake dangantaka da kirki taimako da kuma alheri saboda yawan mutanen day a ke taimako yana daukar dawainiyar rayuwarsu,biyan kudin makaranta kudin aure jari duk tarihin skokoto ba taba samun wanda ya yi irin yadda yake ba,Bad an siyasa ba, bai samo kudinsa gwamnatin sokoto ba, kuma waje ya samo kudin sa ya kuma zo ya bayar, sais hi,
Daya daga cikin matsalar Bashir shine rayuwa mai tsada gaske. Wanda komai nasa yana son yaga yayi na musammam ne, da yawan yawon bude ido kasashen duniya kuma duk inda zai shiga komai nasa na musamman ne, wanda kuma sai ya dubi mafi tsadarsa yake dauka yayi amfani dashi, in otalne yana kwana mafi tsada ne. sannan duk inda zaije yana tafiya ne cikin gungun abokai wanda kuma yada yake rayuwa mai tsada hake yake daukar nauyinsu.zaka ga duk inda ya shiga yana tafiya da tawaga kai kace wani sarki
Ya fara sanin ya shiga matsala daga faduwar hannun jari wanda ya shafi duk harkokin duniya baki daya,wanda yawan kudinsa wanda yake dasu ake juya masa a kasuwannin hannun jari daban daban na duniya, kuma dasu yake biyan kudin da abnki ke binsa bashi. Kasuwar ta ruguje kuma jarin ya rushe.
Matsayin wanna jarinsa a kasuwannin duniya ya kai mataki na na biliyan goma ya koma mataki na uku, kamar kace mutum yana da jarin naira biliyan goma jarin ya koma naira ukku.Matsalar ta kara yawa lokacin day a fara neman diyar shugaban kasa da aure, wanda ya rika yi mata kyauttuttka na fitar hankali, kuma ita taji tana sonsa, don yaro ne da gari abokin tafiyar manya.
Wannan yasa abokan takararsa da kuma suka fara kunna ma duk harkar kasuwancinsa wuta can da can.ya zamana kafin kace me duk katafaren gidajenn shin a Abuja da legas bankuna suka rike a mtsayin garkuwa koda kasuwancinsa ya samu matsala.
Abokan kasuwancinsa , sun fara jin yana jin yayi girma kuma ya fara fuka fukai , yana wasu take take na raina su don haka suka fara jin cewa ya kamata su koya masa hankali. Don haka sai suka fara daukar masa . Ance abokansa suka fara zuga shi cewa shima ya shigo gari. Kuma dai dai yake da kowa,wanna ya sa wadancan tsohon hannun suka ce ya kamata su gwada masa sufa tsaffin jinni kuma tsaffin hannu.An ce sun cunno masa wuta a wurare daban daban wanda in ya taushe nan can ta bude,
Lokacin tona asirin wadanda ake bi bashin banki basu biya ba,bayyana ana bin Rahamaniya bashin naira sama da bilyan arba in daga bankuna wanda bai biya ba. Kuma aka sa shi cikin jerin sunayen masu taurin bashi,wanda ake so yai maza ya maido ko ya fusaknci fushin hukuma,
Bincikenmu ya tabbatar cewa soyayarsa da diyar shiga shugaban kasa tai masa amfani wanda bai fusakanci cim fuska da zarafi kamar wasu.an daga masa har ya yi bayani kuma ya samo mafita.kirkinsa ya sa yana cikin wadanda aka fi yi ma addu a akan Allah ya fitar dashi.Matashi ne day a samu dama Wadda saboda gaskiayarsa a sana a ya sameta,amma karancin shekaru.karancin ilmi addini kona boko.yan fada suka so su kaishi.ko sun baro shi?OHO!