Murtalan Jikin Naira 20: Cikar Shekaru 40 Da Rasuwarshi

0

Daga ISB Daurawa

Murtala Muhammad ya na xaya daga cikin shugabannin Nijeriya da ba zai yiwu a manta da su ba. Matashin shugaba xan shekaru 37, an yi mishi kisan gilla a ranar 13 ga watan Fabrairu, shekaru 40 kenan cur da su ka gabata; a wani shirin juyin mulkin da ba a yi nasara ba, qarqashin shirin Laftanar Kanar Buka Suka Dimka.

Duk da an xauki shekaru da yin wannan xanyen aiki na kashe Murtala, amma jimamin rashinshi bai gushe ba a tsakanin sojoji da farar hula. A shekarar bara ta 2015 lokacin da Murtala Muhammad ya cika shekaru 39 da rasuwa, tsohon shugaban qasa Goodluck Jonathan ya wallafa a shafinsa na ‘Facebook’ dangane da shi kamar haka:

“A yau gwarzo cikin gwarazan Nijeriya Murtala Muhammad ya ke cika shekaru 39 da rasuwa wanda ya sadaukar da ranshi saboda qasar nan. A yayin da ya ke raye, shi ne ya tabbatarwa da duniya cewa Nijeriya fa uta ce gwiwar Afrika. Mu na godewa Allah cewa ba a manta da irin tarbiyyar wannan namijin duniya ba, an yi rubuce rubuce a kansa ta yadda masu tasowa za su yi koyi don gina qasa. Allah ya jiqanshi, tare da dawwamar juriyan rashi a zukatan iyalanshi da sauran ‘yan qasa.”

An haifi janar Murtala Ramat Muhammed ranar 8 ga watan Nuwambar shekarar 1938 a garin Kano, ya yi karatu a kwalejin Barewa da ke Zaria.

A shekarar 1959 ya shiga aikin soji, inda ya yi karatu a makarantar sojoji ta Royal Military Academy ta Sandhurst da ke Burtaniya.

Janar Mutala ya samu mukamin Laftanal a shekarar 1961. Gabanin komawarsa Nijeriya a shekarar 1962, ya je rangadin aiki a qasar Kongo a matsayin wani wakilin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar xinkin duniya.

A shekarar 1964 ne a ka ba shi muqamin Manjo na wucin gadi, bayan da a ka ba shi ragamar kula da sashin sadarwa a hedikwatar rundunar soji ta Kaduna.

Janar Murtala ya koma Lagos inda ya zauna tare da kawunsa Alhaji Inuwa Wada a lokacin da ya zama ministan tsaro, kuma ya kasance a can har lokacin da a ka yi juyin mulki na farko a shekarar 1966.

Shugaban qasa manjo janar Aguiyi-Ironsi ya qara masa girma zuwa Laftanal Kanal duk da kuwa shi ma wannan qarin girma na wucin gadi ne, a watan Afrilun shekarar 1966.

Bayan juyin mulki na farko, sau uku janar Murtala ya na neman haxa kan sojojin arewa da ke Legas domin a yi juyin mulki na biyu, sai dai wannan yunquri bai yi nasara ba sakamakon harbe wasu sojoji da a ka yi a Abeokuta.

Janar Murtala Ramat Muhammed ya taka rawar gani a yaqin basasar da a ka yi a shekarar 1967 lokacin da Laftanal Kanal Ojukwu ke neman valle yankin Biyafara daga cikin tarayyar Nijeriya.

A wancan lokacin janar Murtala ne ya jagoranci rundunar sojin da su ka murqushe sojojin Biyafara tare da kawo qarshen yaqin basasar kamar yadda ya bada sanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar 1967.

Ya na matsayin Birgediya ne sojojin da su ka yi juyin mulki na uku a Najeriya su ka naxa shi a matsayin shugaban qasa , inda a watan Janairun shekarar 1976 a ka qara masa girma zuwa janar mai anini huxu, wato qololuwa kenan.

Har wa yau a wannan lokaci ne janar Murtala ya qirqiro da sabbin jihohi 7 waxanda su ne Neja, Bauchi, Gongola, Benuwai, Ogun, Imo da Bendel. Sannan kuma ya bayyana buqatar mayar da babban birnin Najeriya zuwa Abuja da kuma alqawarin miqa mulki ga farar hula a shekarar 1979.

Kisan Janar Murtala Muhammad al’amari ne wanda ya girgiza Nijeriya, domin kuwa al’umma sun tsinci kawunansu a karo na farko an halaka shugaban qasa me mulki. Janar Murtala Muhammad ya na xan shekaru 38 a duniya a lokacin da a ka aikata mishi wannan xanyen aiki.

Idan akwai wani lokaci da Nijeriya ta samu shugaban qasa mai tsantseni a zamanin mulkin Murtala ne. tarihi ya adana cewa Janar Murtala Muhammad a dukkan kwanakin da ya yi a kan karagar mulki daga ranar 29 ga watan Yulin 1975 har zuwa ranar da a ka kashe shi, bai tava fita da wata mota ba face wata baqar marsandi ta ofis, kuma bai xiban zugar ‘yan rakiya, daga shi sai dogarinshi da direba da kuma odili.

Wannan rayuwa mai sauqi da arha da marigayi shugaban qasa Murtala Muhammad ya yi ne ya bayar da dama a ka iya kashe shi ba tare da wahala ba. a ranar da za a yi mishi kisan gilla, an bayyana cewa Murtala Muhammad ya fita ne tare da dogarinshi Laftanar Akintunde Akinsehinwa da diraba da odilinshi wanda ke xauke da qaramar bindiga.

A ranar da a ka kashe Janar Murtala an shirya musu maqarqashiyar kisan su uku ne, da shi da mataimakansa mutum biyu domin komi ya tafi dai dai. Mutum biyun da a ka so kashewa a ranar da a ka kashe Murtala su ne, mataimakin Murtala xin wanda a lokacin shi ne shugaban ma’aikata Janar Obasanjo, da kuma shugaban sojoji laftanar Janar Theophilus Xanjuma. Dukkansu biyun sun tsallake wannan maqarqashiya, ban da marigayi Murtala.

Kwatsam! Da a ka samu tabbacin kisan Janar Murtala, sai laftanar Kanar Dimka ya garzaya zuwa gidan rediyon tarayya na NBC inda ya yi shela kamar haka; “Ya ku ‘yan Nijeriya, bisa la’akari da gazawar Murtala Muhammad, wasu zaqaquran matasan soji sun kifar da gwamnatinshi.”

Duk a tsammanin Dimka juyin mulkinsu ya tafi kamar yadda su ka shirya ne, har ma ya na umurtan gwamnonin soja da ke jagorancin jihohi 19 da a ke da su a lokacin a kan su sauka a kujerunsu. Shi kanshi Dimka bai rayu ba ballantana haqarshi ta cimma ruwa.

A na tunawa da Janar Murtala saboda namijin qoqarin da ya yi wurin yaqi da cin hanci da rashawan ma’aikata, wanda a zamaninsa sai da ka sallami ma’aikata dubu 10,000 waxanda a ka kama dumu – dumu laifukan cin hanci.

Tunawa da salon rayuwar marigayi Murtala Ramat Muhammad zai taimaki shugabannin Nijeriya wurin kwaikwayon samfurin yadda shugaba ya kamata ya zama. Daga cikin abubuwan da ya kamata shugabanni a Nijeriya su kwafo daga gare shi sun haxa da tsaurin da ya ke da shi a kan aiki, juriya da kuma rashin tsoro.

Idan a ka kwatanta shekarun Janar Murtala da sauran shugabannin qasan da su ka gabace shi, za a ga cewa ya yi mulkin Nijeriya ne ya na da qananan shekaru; shekara 37 a duniya.

MUHIMMAN ABUBUWA 13 DA BA A SANI BA DANGANE DA SHI

Da yawan ‘yan Nijeriya ba su san wanene Murtala Muhammad ba, kawai dai an sunshine a jikin kuxi Naira 20, sai kuma abubuwan da magabata su ka faxi wa ‘ya ‘ya da jikoki dangane da wanene shi. Saboda wannan dalilin ne LEADERSHIP HAUSA ta tattaro muhimman abubuwa guda 13 waxanda ya kamata a sani dangane da Murtala. Su ne kamar haka:

 1. An haifi Murtala Muhammad a ranar talata, 8 ga watan Nuwamban 1938, a jerin gidajen Kurawa da ke cikin birnin Kanon Dabo. Sunan Mahaifinshi Risqua Muhammad, mahaifiyarsa kuma sunanta Uwani Ramatu. Su takwas ne a gidansu, mace guda da maza 7. Kuma Murtala Muhammad ne na biyu.
 2. A ranar 26 ga watan Janairun 1952, a ka xauki Murtala a matsayin xalibi na 941 a kwaleji, Kwalejin da a ka assasa ta a shekarar 1909. Ya na xaya daga cikin xalibai 10 da su ka je makarantar daga Kano. Xaya daga cikin abokan karatunsa shi ne marigayi Muhammad Shuwa, wanda ‘yan bindiga daxi su ka harbe shi har lahira a gidansa da ke garin Maiduguri a watan Nuwamban 2012.
 3. Murtala ya halarci wata makarantar horas da soji a qasar Ghana wacce a lokacin a ke kiranta da ‘Regular Officers Special Training School, ROSTS’, wacce a yanzu a ka sauyawa suna zuwa ‘Ghana Military Academy. A can ne Murtala ya fito a matsayin mataimakin Laftanar. Obasanjo da Gowon duk sun yi wannan makarantar.
 4. Murtala soja ne kaifi xaya, amma fa a wurin iyalinshi mutum mai sauqin kai. A shekarar 2006 matarshi Hafsat Ajoke Muhammad, wacce bayarabiya ce, ta bayyana cewa; “A gida da wurin aiki, mijina ba shi da bambanci. Kamar yadda bay a baki biyu a wurin aiki, haka ma a gida. Mutum ne mai dattako da sanin ya kamata.”
 5. Ko kun san, Kawun Murtala ne ya yi sanadiyyan haxuwarshi da matarsa Hafsah? Bayan da kawun na shi ya haxa su, su ka fara soyayya, haxuwarsu ta farko a jihar Kaduna ne, a can ne kuma Murtala ya sanar da ita burin zuciyanshi har ta kai ga an xaura musu aure a shekarar 1963 bayan ta kammala karatunta, kuma a wannan shekarar ne dai ya kai muqamin Kaftin a gidan soja. A shekarar 1965 Allah ya albarkace su da xiya mace, wacce daga bisani ta yi karatu a kwalejin sarauniya ‘Queens college’ da ke Yaba a jihar Legas.
 6. A lokacin da a ka yiwa Murtala kisan gilla, xiyarsa Zalihatu ta na ‘yar shekara biyu da haihuwa, ita kuma xiyarsa Jummai ta na ‘yar jinjira.
 7. Bayan an kashe Murtala, yayin da labarin ya iso ga matarsa Hafsah, a take ta yanke jiki ta zube a qasa cikin kuka da jimami, wanda hatta waxanda su ka kawo labarin sai da su ka firgita bisa tsoron halin da za ta iya faxawa.
 8. Ya zuwa yanzu dai matar Murtala, wato Hafsah Ajoke tsufa ya kamata, a na matuqar ganin qimarta a qasar nan, saboda duk da kasantuwarta matar shugaban qasa a wancan lokacin, ba ta yi xagawa da wuce gona da iri ba. Allah ya albarkaci aurenta da Murtala da ‘ya ‘ya shida, su ne; Aishat, Fatimah, Zakari, Risqua Abba, Zalihatu, da kuma Jummai. Gabaxayansu sun yi aure.
 9. Ko kun san a  qarshen 1964 ne Murtala ya kai matsayin Manjo (amma na wucin gadi) ‘T/Major’.
 10. Yaqin basasan da a ka yi a Nijeriya wanda ya xauki watanni 30 a na gwabzawa (1967 zuwa 1970), Murtala na daga cikin waxanda su ka fuskanci wannan gumurzu daga farko har zuwa qarshenshi.
 11. Da yammacin ranar 30 ga watan Yulin 1975, Murtala Muhammad ya gabatar da jawabi ga ‘yan qasa a matsayinsa na sabon shugaban qasa, kuma babban kwamandan askarawa.
 12. Murtala Muhammad ne ya samar da wani kwamiti wanda mai shari’ah Ayo Irikefe domin samar da qarin jihohin Neja, Bauchi, Gongola, Benuwai, Ogun, Imo, da Bendel a watan Disambar 1975. Kwamitin kuma ya zo da rahoton da a ka yi amfani da shi wurin samar da sabbin jihohi a shekarar 1976.
 13. Murtala namijin gaske ne, dakakke kuma marar tsoro. Sojoji ‘yan uwansa sun shaide shi da cewa bai san wargi ba, kuma ba ya amsan wargi balle ya yi wasa da mai kawo wargi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here