Rayuwa Cike Da Aminci: Kasashe 20 Da Su Ka Fi Zaman Lafiya A Duniya

0

Daga Idris Sulaiman Bala

Cikin rayuwar fargaba da taraddadin da duniya ta tsinci kanta, kusan kowanne sassa na duniya na fama da barazana daya zuwa biyu na ta’addanci, barna da keta haddin dan Adam. A }asashen turawa musamman yammacin duniya, irinsu Amurka, haka nan wani katon zai bushi iska ya je kasuwa ya siyo bindiga me sarrafa kanta irin ‘yar libarbar din nan ko me jigida, ya shiga kasuwa ko wurin ibada ya yi ta sakin wuta.

A kasashen bakake kuwa; musamman ma marasa kan gadon gaske irin Afrika ta Kudu, babbar damuwarsu a rayuwar duniya ita ce bakin ciki da hassadar ‘yan kasashen waje (‘yan Afrika), don haka ga wanda ya tsinci kanshi a kasar Afrika ta Kudu akwai yiwuwar ya wayi gari wasu zauna garin katti sun kunna mishi taya.

A wasu kasashen Afrikan kuma irinsu Nijeriya, Somalia, Libiya, Masar, Tunusiya da sauransu, kyankyasassun ‘yan ta’adda ne wadanda ke lullubewa a rigar addini, su na kisan kan mai uwa da wabi, saboda tsabar rashin imani da dadi­ kisa.

Saboda yawaitar fashe fashen bama bamai da harbe harbe ne, ya sa masu yawon bude ido su ka tsani wasu kasashe a yankin Asiya. Haka nan za ka iya zuwa kasar Pakistan ko Afghanistan ‘yan ta’adda su yi maka maraba da harsashhi. Ko kuma ka shiga kasuwa bom ya rutsa da kai. A kasar Indiya kuwa, dole sai dai mace ta yi taka tsantsan, saboda akwai kattin bakin hanya masu yiwa ‘yan mata fyade.

Saboda haka dole mutane na bukatar sanin kasashen da su ka kece saura a zaman lafiya; wuraren da za ka je ka more rayuwar cikin aminci, a natse ba tare da fargabar kyafta ido ba. Tun a shekarar 2007 wata cibiya mai suna’ Global Peace Inded’ tare da hadin gwiwar ‘IEP’ su ke aikin bin diddigi tare da tantance wadannan kasashe. A wannan rahoton za mu yi nazarin kasashen kamar haka:

 1. KASAR DENMARK

Ita ce kasar da ta yiwa kowacce fintinkau a fannin zaman lafiya, kwanciyan hankali, da more rayuwa cikin aminci ba tare da wani fargaba ko tashin hankali ba. Saboda tsabar zaman lafiya irin na kasar Denmark, hatta a lokacin yakin duniya na biyu, mayakan Nazi sun mamaye babban birnin kasar wato Copenhagen, wannan bai sa an yi yaki a Denmark ba. Bincike ya tabbatar da cewa mutanen kasar Denmark babbar damuwarsu ita ce bunkasa harkar kasuwanci da tattalin arzikin kasa, a maimakon jefa kawunansu cikin rikici rikici da tayar da zaune tsayen da a ke samu a wasu kasashen. Mutanen kasar Denmark sun iya mu’amala, ga su da taimako. Idan dai ka na da hannu da shuni kuma ka na son zuwa kasar da za ka natsu cikin aminci, to ka nufi Denmark kawai.

 1. KASAR NORWAY

Mutane da yawa za su yi mamakin ganin kasar Norway a cikin jerin kasashe masu zaman lafiya a duniya. Saboda da yawa an san da labarin kisan gillar Anders Behrin Breibik wanda ya girgiza duniya kuma a kasar ya auku, amma duk da haka cbibiyar tantancewa ta fid da cewa kasar Norway na cikin kasashe masu zaman lafiya, ‘yan kasar na da son mutane, ga kawaici, kuma wuri mai aminci ga baki. Duk duniya babu wata kasa da ta kai Norway yawaitar ci gaban ‘yan kasa da gina su. Haka kuma gwamnatin kasar abu na farko da ta  fi muhimmantawa shi ne zaman lafiya.

 1. KASAR SINGAPORE

Duk da kasantuwar kasar Singapore karamar kasa, ba ta sako sako da harkokin tsaro da kare rayukan ‘yan kasa da baki. Tun bayan samun ‘yancin kai da ta yi a shekarar 1965, babban hankoron kasar shi ne sanya kauna da shaukin juna a tsakanin ‘yan kasa, tare da yin maraba da baki.  Singapore na da wadatar arzikin kasa, sannan kuma ga karancin ayyukan barna da ta’addanci. Idan ka ziyarci Singapore za ka ji dadinka yadda ya kamata.

 1. KASAR SLOBENIA

Ta na cikin kasashe masu kyawu da kayatarwa a yammacin turai, Slobenia ma na daga cikin jerin kasashe masu tutiya da zaman lafiya a duniya. Majilisar dinkin duniya ta rattabawa kasar shadar kasar da ke da karancin mabarnata, ga tsaro wadatacce, ga kiyayewa tare da kare hakkin ‘yan kasa. Akwai garuruwa masu dadin sha’ani da saukin rayuwa, ga wuraren yawon bude ido irinsu Maribor da Ljubljana. Garin dadi na nesa.

 1. KASAR SWEDEN

Daya daga cikin kasashe masu armashi kenan, kasar ta na can nesa da arewacin yammacin duniya. Duk da kasantuwar kasar Sweden daya daga cikin manyan kasashen da su ka fi sana’ar makamai a yammacin tura, kasar na da karancin ‘yan fashi dubu 9,000 a shekara idan a ka kwatanta da kasar amruka da ke da yawan ‘yan fashi dubu 350,000. Ba a taba samun wani rikici ko tashin hankali mai kamari a kasar ba, wannan ya sa duk wani mai shaukin zaman lafiya ke sha’awarta.

 1. KASAR ICELAND

Kasashe mai wuraren yawon bude ido, it ace kasar da ba a taba watsa ta a kafafen watsa labarai da sunan rahoton barna, ta’addanci ko tashin hankali ba. Masu yawon bude ido na  zuwa Iceland ne domin ganin irin duwatsu da tekunan da Allah ya fuwace musu. Idan mutum ya ziyarci babban birnin kasar wato Reykjabik zai gaskata kasantuwarta cikin jerin kasashen da ke zaune lafiya.

 1. KASAR BELGIUM

Cibiyar ta ce kasar Belgium na daga cikin kasashen da idan ka ziyarce su a yammacin turai ba za ka so ka bar ta ba. Kasar ta na tsakiyan yammacin turai ne. sunan babban birninsu Brussels, a can ne kuma hedikwatar NATO DA EU su ke. Babu rahoton yawan kashe kashe a kasar, duk kuwa da cewa akwai ‘yar hatsaniya da a ka samu a cikin gwamnatin kasar a tsakankanin shekarar 2008 zuwa 2011. Belgium akwai dadi.

 1. KASAR CZECH REPUBLIC

Duk da kasantuwarta sabuwar kasa, Czech ta samu ‘yancin kai ne a shekarar 1989 bayan da a ka yi juyin Belbel. Bayan wannan samun ‘yancin kai babban abun da kasar Czech ta sa a gabanta shi ne gina kasa, gina rayuwar al’umma, gina amintaccen tattalin arziki da kuma hannun jari ga baki. Jin dadin rayuwa da kauracewa tashin hankali sai ka ma ziyarci babban birnin kasar, wato Prague.

 1. KASAR SWITZERLAND

Kamar yadda cibiyar IEP ta bayyana, kasar Swiss ta yi sa’ar kiyaye abu guda, shi ne gwamnatinta ba ta gargada, haka kuma siyasarsu cike ta ke da ‘yanci. Saboda haka ne kasar ta yi kaurin su na wurin zaman lafiya, da karancin bangar siyasa, haka kuma ba a samun kakkausan suka da fada a tsakanin ‘yan siyasan, wanda wannan ya taimaka sosai wurin tabbatuwar zaman lafiya.

 1. KASAR JAPAN

Idan dai a na maganar kasar da ta kece tsara ne wurin kiyaye al’ada, dole a fara da Japan. Kasa ta uku mai yawan tattalin arziki a duniya. A na zaman lafiya sosai a Japan, babu barna sosai, babu rikicin kabilanci. Kowa harkar gabanshi ta dame shi. Wani abun sai ka je can.

 1. KASAR IRELAND

Tarihi ya shaidi kasar da yalwar kasar noma, wuraren tarihi da kuma al’umma mai dadin mu’amala. Duk mai shaukin yawon bude ido dole yay i sha’awar Ireland, saboda babu fargabar kwabo da za ta dame shi. Maziyarta na tururuwar ziyartar Ireland a duk karshen shekara.

 1. KASAR FINLAND

Kasashe ta wayayyu wadanda su ka san zamaninsu da duniya yadda ya kamata. ‘yan kasar ba su fiye zafin kai ko aikata barna  ba. Zaman lafiya ya wadata a Finland, ‘yan kasuwa da maziyarta na morewa a garuruwan kasar. Wani karin haske dangane da kasar Finland shi ne yadda gwamnatin ta muhimmanta batun ilmantarwa, wannan ya taimaka sosai wurin isar da sakon zaman lafiya da wanzuwarshi.

 1. KASAR NEW ZEALAND

A kowacce shekara tun daga shekarar 2007 sai sunan New Zealand ya shigo jerin kasashen da su ka fi kowanne zaman lafiya a duniya. An tabbatar da cewa ‘yan asalin kasar New Zealand kaso kalilan ne ke garkame a kurkuku, saboda babu yawan barna a tsakaninsu. Mutane ne masu son zaman lafiya, taimako da kuma tarairayar baki.

 1. KASAR CANADA

Mutanen kasar Canada sun fi mutanen kowacce kasa morewa rayuwa a duniya. Yawan mutanen kasar ya kai miliyan 33, amma kuma it ace kasa ta biyu da ta fi kowacce fadin kasa a duniya. Garuruwan da ke kasar Canada masu tsafta ne, ga ado da kawa, ga mutanen kasar da kaunar baki da son juna. Idan ka ziyarci Canada ba ruwanka da fargabar dan fashi, ballantana kuma dan bindiga dadi ko me kona mutum da tayar mota.

 1. KASAR BHUTAN

Dalilin da su ka sa a ka sa kasar Bhutan cikin jerin kasashen da ke da zaman lafiya shi ne yadda kasar ta tsere saura a fannin rashin aukuwar tashe tashen hankalu a cikin shekaru shida cur, ko ina a cikin kasar shar, babu barna barkatai, akwai karancin karya doka da oda, ya na da wahala ka ga soja a ciin gari, ‘yan sanda ba su yawo da bindiga, kafin ka ga bindiga a Bhutan za ka dade. Wannan duk zaman lafiya ya haifar da su.

 1. KASAR AUSTRALIA

Kasashe ce me kyau da fasali, ga zaman lafiya a tsakanin kabilunsu. Yawaitar al’adu a kasar Australia ba shi ya hana su kaunar juna da mutunta al’adun juna ba, tare da kiyaye martabar baki. Kasar ta na da girman kasa duk da yawan mutanenta bai wuce miliyan 20 ba. A na zuwa yawon bude ido kasar saboda wanzuwar zaman lafiya.

 1. KASAR PORTUGAL

Abun mamaki kenan, amma kuma fa ba wani abun mamaki can ba ne, saboda ita kasar Portugal ta haura shekaru 26 a matsayin member EU ba tare da aikata wani laifi ko saba doka da ka’ida ba. Wannan a jininsu ya ke; dabi’ar ‘yan kasan ne bin doka, kiyaye oda da ka’idoji. Haka kuma mutanen kasar sun san mutuncin kawunansu da na baki. Don haka hankali kwance za ka je Portugal ba tare da wani dar dar ba.

 1. KASAR KATAR

Garin dadi na can nesa da mu, bincike ya tabbatar da cewa duk fadin gabas ta tsakiya babu kasar da ta kai kasar Katar zaman lafiya da kwanciyan hankali. Ba a samun rahotannin fargaba da tashin hankali kamar yadda a ke samu a wasu kasashe. Haka kuma ‘yan kasan an ba su ‘yancinsu, hatta mata babu wata doka da ta yi wa hakkokinsu Karen tsaye. Wannan ‘yanci da a ya wadata a Katar ya sa mutanen kasar na yiwa baki tarba ta musamman tare da kiyaye aikata ayyukan barna.

 1. KASAR MAURITIUS

Kamar yadda rahoton cibiyar GPI na shekarar 2013 ya bayyana, kasar Mauritius ta na daya daga cikin kasashen da ke zaune cikin lumana a duniya. Kasar Afrika da ta fi kowacce zaman lafiya. Kasar ta fid da kasashen Afrika kunya, wadanda a kullum sai fadadawa su ke yi a ayyukan rashin mutunci da tayar da kayar baya. Lallai Mauritius wurin zuwa ne don a sakata a wala.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here