Shekara Daya Da Rasuwar M.D Yusufu: Bankwana Da Kundin Tarihi Mai Rai

0

Daga Danjuma Katsina

Makabartar dan Takum da ke  birnin Katsina, ta samo asali ne daga wani malami masanin addinin musulunci kuma waliyyi mai suna Muhammad Ibn Ahmad At-Tazakhat. A nan ne a ka rufe M.D Yusufu, a gefe da kabarinsa. Daga hannun dama kabarin mahaifiyarsa ne mai suna Hajiya Hadiza, wadda ta rasu shekaru 10 da su ka wuce.

Daga hagu kabarin yayarsa ce mai suna Hajiya Akila wadda ta rasu shekaru 20 da su ka wuce. Wajen da a ka rufe shi, shi ya zabi wurin shekaru 15 da su ka wuce. Kuma an ce wani lokaci ya kan kai ma wajen ziyara. Ya na kuma sawa a je ziyar wurin da ya kira sa da sunan gidansa na karshe a duniya.

Daga bakin kabarin idan ka daga kanka sama ta gabas za ka iya hango dakinsa da ke gidansa na Katsina, amma wani dogon bene da a kai ya kare shi. Daga kabarin zuwa gidansa tafiya ce ta ‘yan mintuna a kasa wanda sam ba za su kai mintuna goma ba. idan ma ka tafi cikin kuzari, mintuna biyar sun kai ka.

Gidansa ya na unguwar da a ke kira Yaranci, unguwar da Sarki Dikko ya kafa ta domin ‘ya ‘yansa. Titin da gidan ya ke, sunan kakansa ne a ka sanya masa. Muhammad Dikko Road. Lamba na 49 daga gidan idan ka kalli yamma, ka na iya hangen gidan Mahaifinsa, Magajin gari

Yusufu Lamba.

Gidan M.D Yusufu na Katsina an gina shi da jan bulo. Duk Katsina shi kadai ne gidan da a ka fara ginawa gini cikakke da irin wannan bulon. Ya yi ginin ne da shi saboda shi wuta ba ta cinsa, ga kwari. Ginin bene ne hawa daya, kasan benen bangare daya dakin karatu ne, wanda littafan da ke ciki sun fi na babban laburaren jihar Katsina muhimmaci, wani dakin kuma jaridu ne kala kala na tsawon shekaru, wadanda an yi aikin hada su littafi – littafi, su ma sun cika wani daki.

Sai  dan wajen da ya ke ganawa da mutane, wanda bai iya daukar mutum goma lokaci guda. A saman benen, sashen da ya ke na  sa ne, cike ya ke da littafai, Jaridu  da muhimman takardu. Kashi biyu cikin uku na gidan dauke ya ke da littafai, jaridu da takardu masu muhimmaci.

A gidansa na Legas, tarin littafai, jaridu da muhimman takardu su ne su ka cinye kashi biyu da kwata cikin uku na gidansa. Tirela – Tirela a ka rika cikowa zuwa cibiyar Yusufu Bala Usman da ke Zaria, a lokacin da zai baro Legas da zama kwata –

Kwata.

A gidansa na Abuja tun daga  falonsa, Litattafai da jaridu su ne kewaye da shi, daya daga cikin ‘ya ‘yansa har rasa daki ya yi. Sai dai ya rika rabawa a dakin karatu ya na kwana. A dakunansa littafai ne, jaridu a jejjere a ko ina. Duk wani littafi da ya zo ma sa sai ya karanta shi. Idan kuma ya ji labarinsa zai sa a nemo masa. Kuma ya karanta. Ba wani littafi da a ka rubuta wanda ya shafi Nijeriya ko Afrika da bai da shi, sai dai marubucin idan wani dan dagaji ne.

Idan littafi ya fito, zai same shi, zai karanta. Kuma za ka ji ya na sharhin cewa abin da ya fada haka ne ko kuwa da kuskure. Wani lokaci  za ka ga ya bugawa marubucin waya ya ce na ga littafi kaza. Amma abu kaza da kaza a cikin littafin ba haka ba ne.

Duk wasu muhimman abubuwan da su ka faru a tarihin Nijeriya gabansa a ka yi. Ya na da masaniyar cikakkiyar ya a ka yi, daga kokarin amsar mulki a hannun turawa zuwa Jamhuriya ta biyu. Zuwa juyin mulkin farko na kashe su Sardauna, zuwa na biyu na kashe su Ironsi da yakin Basasa.  Zuwa juyin mulki na tsige Gawon da na kashe Murtala. Da kuma bai wa Obasanjo da mika mulki ga farar hula su Shagari, da amsar su Buhari da amshewar Janar Babangida da Shonekan da Abacha har zuwa Jonathan.

Duk abubuwan da su ka faru gabansa a ka yi su. Ya san ya a ka yi, me kuma a ka yi. Da yadda a ka yi. Idan ku na magana da shi, za ka ji ya ba ka misalai na shekaru  50, ya rika kawo wa daki – daki har a gangaro zamanin da kuke. Sai ya yi sharhi ya kuma fitar maka da misali da mafita.

Ya san tarihin asalin garuruwa, mafi yawan wadanda su ka rike kasar nan  ko  su ke  rike da wani matsayi, ya sansu ya kuma san asalinsu. Wasunsu ya san labaransu kala – kala. Ya na da tattara littafin da a ka rubuta na gida, ko wasu Iyali, ko dai daiku. Wani lokaci idan ya  karanta ka ji ya yi sharhin marubutan sun yi kuskure  ko  dai  dai.

Manyan shehunan ilmin tarihi a kasar nan, sun sallama cewa shi wani tushe wanda za ka san gaskiyar me ya faru a tarihin siyasa da mulkin Nijeriya. Shehunnai irinsu Farfesa  Abdullahi Mahdi BC na jami’ar jihar Gombe. Farfesa Alkasim Abba BC na jami’ar jihar Adamawa da Dakta Abubakar saddik na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, da Dakta Patrick Wilmont. Wadannan kadan daga Shehunnan malaman da su ka sallama masa kenan.

Ba ya tarayya da kowa sai wanda ya san ciwon kansa, ko ya san abin da ya ke yi. Ko mai wata kyakkyawan buri da alkibla. Duk wasu masana da manazarta a kasar nan sun san da zamansa.

See also  HIKAYA DAGA TASKAR LABARAI

Idan kuma ya dauke ka cikin tawagar da ya ke jin za ku yi tafiya tare, ba ya nuna bambanci. Ya kan ce ka koyi mu’amala da manya don wata rana ba sa nan kai kenan.

Na taba samun kaina, mu na mitin a waje guda lokaci guda, ga marigayi Dakta Yusufu Bala Usman, marigayi Farfesa Sam aluko, malam Sani Zorro, Dakta Abubakar sadik. Na kalli teburin na kalli kaina, na kalli wanda ya tara mu, Marigayi Malam M.D Yusufu. Ya faru a shekarar 2002, da jikina ya yi tsam. Sai na dauko biro da takarda. Na rubuta dan wake kamar haka:

In an tambayeki ina ina?

Fada masu, ina a cikin Giwaye

Fada masu ina tsakiyar Zakoki,

Fada masu ina gaban Dakaru

Fada masu na zama Jinjiri a na mani  ta ta ta.

Fada masu ina a wani zama na tarihi.

A gaba na marigayi Uche Chukumeiriji a lokacin ya na Sanata, ya zo a ka zauna a ka tsara yadda za a wargaza shirin da wasu ke yi na kawo tazarcen Obasanjo a majalisar dattawa. Gaba na a ka tsara hatta shahararriyar jawabin da ya yi ma manema labarai, wanda ya ke cewa ‘third term is real’.

Da na ga yadda a ke shigi da fici na ga yadda kwalwa ke aiki. Idan a ka tattauna ko a ka aiwatar da wani aiki., sai a dawo wajen M.D Yusufu. Wani lokaci ka ga ya soke duk tsarin da a ka yi ya sake sabo. Wani lokaci kuma ka ga ya canza masa fasali.  Wani tunani sai ya shige ni. Shi ma na sake wani rubutun kamar haka:

Tarihi ya na aukuwa ne da mutane.

Tarihi ya na faruwa ne da bigire,

Tarihi ya na aukuwa ne da lokaci.

Tarihi  ya na  da ‘yan taka rawa da kuma ‘yan kallo.

A inda ni ke tarihi ne zai faru.

A wurin ina kallo. Ina taka rawa da bayar da ruwan sha da kuma gurzo takarda.

A inda na ke ina daukar darasin da ba wani aji da za a iya samunsa.

M.D Yusufu mutum ne mai karfafa gwaiwar adana tarihi, da bincike a kan tarihin, wannan ya sanya ya sha daukar nauyin asassa  wajen kayan tarihi da bayanan tarihi. Yayi tsaye cak wajen ganin an gina Yusufu Bala Usman centre da ke Hanwa zariya.

Idan ya ba ka littafi zai tambaye ka me ka fahimta. Idan ka kawo masa littafi kyauta zai tabbatar maka ya karanta. Idan akwai abin gyara a ciki ya gyara maka. A gidansa zai a jiye littafi ko wata takarda. Amma zai waya ya ce a duba waje kaza na ajiye shi. Za kuma a ji an ce ya ajiye shi tsawon lokaci.

Idan ya na fadi maka faruwar wani abu na tarihi, za ka ji ya na kawo labarin daki daki kamar yanzu. Lokaci, rana, wata da kuma shekara.

Ya taba bani aron littafi, bayan wani lokaci ya bukaci abinsa. Ina Katsina ya na Legas, ya sanya na je Kano na hau jirgi na kai masa. Ya amsa ya duba ya ajiye shi. Ya ce hau jirgi ka koma gida. Na ce masa, Yallabai, littafin fa naira Uku a ka saye shi. (kamar yadda ya ke a rubuce a jiki). Sai ya ce idan za ka samo min shi na saidawa a kasuwa  zan saya rabin miliyan. Ya ce, ai ba inda za ka same shi ko da nawa ne. kuma idan ba a kula da shi ba, ya za a adana ilmin da ke ciki? Ya ce, ka na lissafin kudin jirgi ne da tasin da ka hau. Ni kuma ina lissafin idan ya salwanta  ina zan samo  shi?  wanda  ya rubuta shi ya mutu. Kamfanin babu shi. ko a lokacin kwafi  500 kacal a ka buga.

A 2013 da na kai masa shawarar  za mu kafa cibiya mai suna M.D Yusufu research and documentation centre. Sai ya kura min idanu. Sannan ya ce  idan kun ga ya dace, to Allah ba da sa’a. Ya ce, ta ku ce? Domin ni tawa ita ce Yusufu Bala Usman centre da ke Zariya. Na ce to kowa ya yi nasa. Masoyanka su taimaka mana. Kai kuma ka nemo mai taimaka maka a taka. Sai ya fashe da dariya.

Aikin da Allah ya sa ma albarka, gwamnatin Katsina karkashin Ibrahim Shema sun bayar da fili a na da kwamitin aikin. Wanda in a ka yi ta za ta zama abin misali da darasi a kasar nan.

Gani na karshe da shi, na je gidan zan je in kwanta. Ya ce na dauko wata mujjala mai suna ‘The Atlantic’, ya ce, je ka karanta da safe mu tattauna a kan labarin da su ka kawo .

M.D Yusufu, ya tafi . Ya tafi ya bar tarihi, jibge a cikin dimbin littattafai da kuma tarin takardun da ya bari. Amma tarihin da ya tafi da shi a kwalwarsa ya na da yawan gaske kuma ya tafi da abinsa har abada.  Allah ya jikansa.

Danjuma Katsina

marubuci ne, kuma dan Jarida.

08035904408, mdanjumakatsina@gmail .com

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here