Tashin Hankali A Zamfara: Kowa Ya Saurara!

0

Daga Sulaiman Bala Idris

Abin dai da ban mamaki, ga kunya, daure kai, da rashin sanin ya kamata. Ni wasu lokutan ma, na kan ji tamkar na daura hannu bisa kai, na yi ta kwala ihu. Da zaran na ji an ce Zamfara, sai hankalina ya kada, zuciyata ta buga ras! Domin na san bai zama dole ya kasance cewa ba labarin garkuwa, ko tarwatsa kacokaf din kauye zan ji ba.

Irin ta’asar da ‘yan ta’adda, mabarnata, ‘yan share wuri zauna suke aikatawa a Zamfara, hankali ma baya dauka. Ta’asa ce da aka ki mayar da hankali a kanta, kai ka ce Kwarin Gona ake kashe wa, ba mutane masu jini da tsoka ba. Mafi ban haushi da lamarin Zamfara shi ne halin ko in kula da manya, wadanda suka fito daga yankin suke nunawa dangane da abubuwan dake faruwa. Sun yi gum! kowa ya rufe bakinshi, alhali hakki ne da rataya a wuyansu na kare rayuka, da dukiyoyin jama’ar da suka zabe su. Idan da manyan mutanen da suka fito daga yankin Zamfara suna yekuwa dangane da irin ta’asar da ake aikatawa al’ummarsu, da zuwa yanzu an san irin matakan da aka dauka.

Ai wasu lokutan, yin shiru a Nijeriya da masu rike da madafun iko ke yi, shi ke bayar da dama ga mabarnata su ci gaba da aikata barna. Duka-duka yaushe ne aka fara kashe mutane a Binuwai? lamari ne da ya fara ‘yana kwanaki kadan baya, kuma duka-duka mutum nawa aka kashe? har zuwa yau ba a kashe sama da mutum 200 a Binuwai ba. Farat daya manyan mutane daga Binuwai suka dau dumi, suka yi ta yayata lamarin, suna barranta da ci gaba da kashe musu al’umma. Sai da ta kai a ko ina a fadin Nijeriya an saurari koken mutanen Binuwai. Sai da ta kai a kowanne lungu da sako na Nijeriya, an san cewa ana kisa a Binuwai. Amma fa kar a a manta, a daidai lokacin da shugabannin al’umma daga Binuwai suka fito don nuna kin jinin kisan da ake yi musu, ana ci gaba da samun kashe-kashe da munana barna a Zamfara.

Abin kunya da takaici, shugabannin al’umma daga wannan yanki na Zamfara, kamar ruwa ya ci su. Ba zan yi jam’i ba, tunda Sanata Marafa ya tabuka wani abu, ya fitar da kansa daga wannan kunya. ko ba komi ya mike a gabana majalisa, ya fitar da abin dake kumshe a ransa na irin bakin cikin da mabarnata suke jefa al’ummar yankin Zamfara. A makon da ya gabata, akwai wani faife na jawabin Sanata Marafa a gaban Majalisa, inda ya fito da wasu abubuwa fili dangane da yankin Zamfara. Marafa, ya fallasa cewa, a daidai lokacin da yake magana a gabana Majalisar, ya samu kiran waya da sanyin safiya daga Mahaifarsa (Zamfara) cewa an yin garkuwa da wasu mutane. Ya ci gaba da cewa, Jihar Zamfara a yanzu na karkashin ikon tsagera da ‘yan bindiga ne. Musamman ma daga mahaifarsa. Cikin abubuwan taba rai da Sanata Marafa ya fadi a gaban Majalisa hard a batun cewa; ‘Gwamnan Jihar Zamfara ya san wadannan mabarnata, mataimakin gwamna ma ya sansu.’ Don karin haske, a gaban majalisar Sanata Marafa ya kara bugun kirji, ya ce, eh, na fadi kuma zan kara fadi, Gwamnan Jihar Zamfara ya san wadannan miyagun da suke ci gaba da kashe mutane a Zamfara. Ba kawai Gwamna da Mataimakin Gwamna ba, a gaban Majalisar Dattawa, Marafa ya ce Kwamishinan ‘yan sandan Zamfara ma ya san wadannan mabarnata dake cin karensu ba babbaka a Zamfara.

Su wane ne wadannan mabarnata? Marafa ya ce ba a boye suke ba, suna yawo a bainar jama’a ba tare da wata fargaba ba. kuma kowa ya sansu. Da makamansu suke yawo. Mafi ban tsoro a cikin wannan ta’asa na Zamfara, Kamar yadda Marafa ya bayyana, shi ne yadda ya zama wadannan mabarnata sune suke yin hukunci da alkalanci a tsakanin al’umma. Mutane sun daina zuwa wurin hukuma ko masarauta don a yi musu alkalanci.

Da zaran an samu matsala, wurin wadannan mabarnata ake zuwa su yi hukunci. Tunda al’ummar Jihar Zamfara sun jima da sallama Gwamna Yari, sun gamsu cewa babu wani abu da zai iya domin tseratar da su daga wannan ta’asa. Toh, tambayar da nake da ita a daidai bigiren nan ita ce; Shin ina sauran zababbu daga Zamfara suke? Ina manyan mutane ‘yan salin Jihar Zamfara suke? Shin baku da labarin cewa makonnin baya kadan aka far wa ’Yar Galadima dake karkashin karamar hukumar Maru, inda aka kashe mutane 152? Haka nan A kauyen Kizara dake karkashin karamar hukumar Tsafe an kashe mutane 58. Ina Sanata Yariman Bakura? Shin bai san cewa a Maradun, karshen makon da ya gabata an kai mummunan harin da aka samu salwantar rayuka ba? Ita kanta Bakurar a cikin hatsari take, haka nan Birnin Magaji, Zurmi da Shinkafi? wa Yarima yake wakilta kuma wa yake kare wa? Shin a haka za a ci gaba da zura ido, ana kisan kiyashi a Zamfara? Wannan ta’addanci da raina rayukan al’umma dole ne a kawo karshensa. Zamfarawa ma mutane ne, ya zama wajibi a kiyaye rayukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here