Yadda Masu Kudi Ke Sarrafa Siyasa Da Zabe: Darasi Daga Alhaji Dahiru Mangal

0

Daga Danjuma Katsina

Shiga siyasa,wani lamari ne dake bukatar kudi.kudi kudi kudi kuma ba kana na ba.kudi wandanda ake kashewa baka da tabbacin dawowarsu. Don baka da tabbacin zaka ci zaben.kudi wadanda makiyanka zai iya fin amfana dasu fiye da masoyanka. Saboda a lissafi ka kana son ka jawo makiyinka ne ya yarda da kai . tunda ka riga ka samu amincewar masoyinka.

Kudi wadanda wadanda zaka maida kanka a sakarai a lokacin da ka ke rabar dasu.kana ji kana gani a mayar da kai baho , amma ka kau da kai. Kuma ka bayar kana dariya kana ka gode. Kudi wadanda zaka bayar da ka san bayar dasu kasan karya ne, kuma yaudara ce. Amma kana ji kana gani ka bayar kuma kace, madallah.

Na yi bincike akan yadda masu kudi ke daukar nauyin siyasa da zabe. Da kuma yadda kudin da suka kashe kan sa suyi tasiri a gwamnatin da aka kafa.ta siyasa.bincike na nayi daya a gwamnatin tarayya akan wannan gwamnatin APC da aka kafa.ta janar muhammadu buhari.
Suwa suka taimaka da naira da kwabo da kuma dala?wane tasiri suke das hi a yanzu a cikin ta? Na kuma yi a kan gwamnatin jahar Katsina.wadda alhaji aminu Bello masari ke shugabanta.bincike na akan gwamntin tarayya. Rubutun sai nan gaba zan kawo shi.

Akan gwammantin jaha Katsina,na tattauna da wasu yan siyasa akan yadda abin ya faru.da wasu manajojin banki da wasu da sun san ya akai me akai.rubutu irin wannan ba a kama suna. Mafi yawan wadanda zasu baka bayani zasu ce kar ka fadi suna na. amma zan shaida maka gaskiyar abin da na sani. Don haka mafi yawan wadanda na zanta da su. Wasu na basu suna ne. amma na sakaya gaskiyar, sunansu; da aka sansu dashi.

Ahmad. Ya fada mani cewa.’’ Kasan mun dade muna takara, kuma mun dade bama aikin komai sai dai dan abin da baa rasa ba. sai kuma yan buga bugaa.sai yan saide sai de don a rufawa juna asiri.a haka muka sake dawowa takara’’
Ahmad na daga cikin yan siyasa da aka yi fadi tashin siyasar masari dashi. Tun tsayawarshi gwamna na zangon farko [2007].kuma har yanzu yana cikin wadanda ake damawa dasu.
Ahmad yaci gaba da cewa siyasa da yakin neman zabe, tsada gare shi. a cikin ba a san babu ba.jami an jam iyya a basu. Jami an zabea basu jami an tsaro a basu.yan siyasa a basu yan banga a basu. Kuma ba wanda zai gudummuwar kudinsa a zabeenka sai ya lura kana hanyar nasara.

Sani ,na daya daga cikin wadanda aka yi . gwagwarmayar dashi. Yace. Mun shigo takara a Katsina. Aljifun mu,fayau.ga zaben fidda gwani.wanda lissafinsa.yana da yawan a tsakanin nera da kwabo. Saboda muna takarar fidda gwani da wadanda .kudi ba matsalarsu bace. Kuma basu wahala ba, kamar mu.ba a sansu ba kamar mu.

Dallatu ya yawa ta neman tallafi. Dan abin da ya samu bai wuce kofin shan ruwa ba. ga muna da lissafin kudi a wajenmu yafi cikar tankin ruwa. Duk in da muka je da kokon bara.a tsakanin yan jam iyyar APC na gaskiya.sun fi damuwa da zaben shugaban kasa.suma sun shagala da zaben inda suke na gwamna.muna ta kawo mafita da tattauna ta.cin zaben fitar da gwani. Shine tabbatar mana da nasarar shiga zaben gwamna.

Apc ta tsara cewa. Zaben za ai gaskiya da gaskiya ne wanda yaci a bashi. .amma gaskiyar Magana kowa ya san dan takara sai ya sayi daliget.da wadanda zasu gudanar da zaben. Haka muka yi ni mu ka kwana cikin fargaba da tsoro.akan me za ayi kuma ina mafita?
Malam mani, ya shaida ma marubucin nan cewa.lokacin da lamari ya kai in taha.ga zaben fitar da gwani na matsowa.sai wasu i [mun sakaya sunansu] suka fara jagorantar wata tattaunar sirri da hamshakin dan kasuwar nan Alhaji dahiru bara u mangal.akan ya dau nauyin zaben bisa wasu ka idoji da yarjejemniyar da za a tsara.

Na samu tattaunawa da wasu da sukayi man ikirarin sun san . duk yadda akayi. Sun ce .an yi tattaunawa a sirrance a lokacin. Saboda Mangal dan kasuwa ne. wanda in ya fito fili gwamnatin dake mulki ta jaha da ta tarayya. Tana iya yi masa illa.wanda a tarihan ce. Duk duk duniya dan kasuwa ba ya taba yarda a yaja da gwamnatin dake bisa mulki. Don haka an rika tattaunawar a sirrince. Kuma bisa alkawalin cewa sirri ne.
‘’mun yi sa ar Mangal baija ba. wurin amsawa don taimaka mana. Don shima a lokacin gwamnatin jahar ta lokacin tana wahalar da duk wata harkar kasuwancinsa da kamfanoninsa suka yi da gwamnatin.ana rike masa kudi. Yana bin basussuka tsawon shekaru anki biyansa.’’inji wani da yace ya san me ya faru.
A lokacin ‘’ ba karamar tarar aradu da ka kuma ba karamar zunguro sama da kara Mangal yayi ba wajen amsa cewa.zai bayar da abinda ake nema ya cimma gaci don kamar ace soja ne ya sa hannu ne ga takardar shirya juyin mulki.’’inji alhaji sa ad.wanda yace shima yasan wani abu akan zaman.

Ahmad ya kara man cewa. Mangal ya amince bisa wani tsari ya fara daukar nauyin takarar fidda gwani .shigowarsa ta canza duk fasalin yakin neman zaben. Hankalinmu ya kwanta.da kudinsa muka ci zaben fitar da gwani da kuma kudinsa muka je babban zabe.’’
Alhaji sa ad. Yace a lokacin da za a tafi Babban zabe, gwamnatin Katsina karkashin Pdp na da sama da naira bilyan hamsin a cikin asusunta.kuma a shirye take ta watsar dasu don taci zabe.duk attajiran Katsina da yan kwangilarta PDP suke . wadanda basa tare da gwamnatin suna jin tsoron bada wata gudummuwa mai yawa.sun dan bayar .amma wanda ya san yadda zabe ke lakume kudi yasan dan abin da suka bayar sai dai a sha ruwa.

Na tambayi wasu daga cikin manajojin bankin da mangal ke hudda da su.sunce mani kaidar aikinsu sirri ne. basa bayyana fitar ko shigar da kudi.bincike na ya tabbatar man cewa a kwai lokacin da akwai lokacin da aka fitar da bilyan biyu a tsakanin wasu bankuna ciki kwana ki uku kacal .

Bincike na ya tabbatar man. Shigar mangal daukar nauyi zaben da ya gabata a jahar Katsina. shine. Nasarar masari a zaben fidda gwani. Da APC a matakin jaha da tarayya.a matakin jaha.

Danjuma Katsina. Marubuci ne kuma dan jarida. 08035904408 email. Mdanjumakatsina@gmail.com twiter .@danjumakatsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here