Yaron Da Ya Fi Kowa Wayo Da Hazaka A Duniya

0

Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

A kullum a wannan duniyar matukar ba barinta mutum ya yi ba, ma’ana rai ya yi halinshi, ka yi ta ganin ababen al’ajabi da mamaki kenan. Duk lokacin da a ka samu sauyin zamani, sai abubuwan al’ajabi sun ninka.

Idan a shekaru 200 da su ka shude za ka cewa mutum nan gaba za a samu ci gaban da Idan ka na da kudi za ka cilla wata duniyar yawan bude ido, a wancan lokacin za su ce ma wannan aiki ne na aljannu ko Mala’iku. Amma a yanzu zuwa wata duniyar ba wani labarin a zo a gani ba ne. Duk kauyancin mutum ya san a kan je wannan shawagi.

Haka nan kuma zamanin na kara ci gaba ne, mutane ma na kara ci gaba da samun yalwar kwakwalwa. Basirar al’umma na sake bayyana. Idan mutum ya aikata wani aikin, hatta aljannu sai sun yi kishinshi.

Bayyanar wani yaro me suna Joshua Beckford ta yi matukar motsa tunanin al’umma musamman ma kaifin hazakarshi da wayo. A yayin da kananan yara ‘yan shekara 8 walau su na firamare ko kananun azuzuwan sakandare, ko kuma su na gararanba a gari abinsu.
Shi kuwa yaro Joshua wandaya kafa tarihi a duniya ta hanyar fara karatu a babbar jami’ar Odford ya na da shekaru 6 sai da ta kai an shelanta sunanshi a cikin kamfen din ‘National Autistic Society’s Black and Minority’

Yaro Joshua ya shiga kundin tarihin duniya, ta yadda hatta karatun su firamare da sakandare a gida a ka yi mishi su, saboda hazakarsa ta girmi ta shiga aji dai dai da yara’yan shekarunsa.Ya yi fice a fannonin lissafi, falsafa, harsunan kasashe, tarihi, kimiyyar kwamfuta da fasaha.

Wani farfesa a jami’ar City ya bayyana cewa Joshua shi ne yaro da ya fi duk wani yaro hazaka da wayo a duniya.

A shekaru 8 ya yi nisa a fannin ‘neurosurgery’ kuma ya na tsananin yin abubuwan ban mamaki da al’ajabi. Haka kuma yaro ne da ya bayyana cewa ya na da muradin sanin Ilmin taurari, sannan ya ce ya na matukar son fadada bincike dangane da tarihin kasar Misirah.
Allah daya gari bamban. Allah be kadai ya san me wannan hazikin yaro zai zama a shekaru masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here