Kowa Dan Nijeriya Yana Da Rawar Takawa Don Yakar Kalaman Batanci

0

Shugaban kungiyar bunkasa ci gaban fasahar sadarwa mai suna CITAD tace kowane dan Najeriya na da rawar da zai taka domin samar da zaman lafiya cikin kasa.

Shugaban na kungiyar ta bunkasa ci gaban fasahar sadarwa mai suna CITAD da ke bibiyar kalamun batancin da ake yayatawa a kafofin yada labarai da kuma na sada zumunta, yayi bayanin cewa kalamun batanci masu nasaba da addini da kabilanci sai karuwa suke yi a cikin al’umma.

Cibiyar tayi wannan bayanin ne a wani taron data gudanar a Bauchi na masu ruwa da tsaki musammam masu mu’amala da kafofin yada labarun da suka hada da ‘yan siyasa da kuma ‘yan jarida.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here