Hangen Na Sama Ya Kawo Lalacewa Aikin Gwamnati – Isa Katsina

1

Daga Kabir Ahmed S Kuka

Jahar Katsina ta yanzu na daya daga cikin yankunan arewacin Najeriya wadda ta kyankyashe ma’aikata wadanda suka yi suna ba a Najeriya kadai ba hadda kasashen waje. Kusan babu wani sashe na aikin gwamnati wanda dan jahar Katsina(tun ana kiranta da lardi koma kafin lardin) bai sa hannunsa aciki ba walau na tsaro ko zaman ofis. Wakilin Aminiya na jahar Katsina yaci karo da daya daga cikin irin wadannan tsaffin mai’aikata wanda ya fara aikin gwamnati bayan shekaru biyar da samun ‘yancin kan Najeriya.

Aminiya – Ko zamu ji takaitaccen tarihinka?

Alhaji Isa Katsina – Assalamu alaikum. To da farko dai sunana Isa Muhammad Katsina wanda akafi sani da Isa Katsina. An haifeni a ranar 24 ga watan Satumba na shekarar 1940 acikin garin Katsina. Na fito daga tsatson wani bawan Allah wanda ake kira Magaji Rogo Abdullahi Jabo. Kamar kuma yadda aka sani a al’ada ta mutanan Katsina ta fara kai yaro makarantar Allo domin fara samun ilmin bautar Allah,to nima mahaifina Malam Ma’azu Allah ya jikansa da rahama baiyi kasa agwiwa ba wajen sabke wancan nauyi. Ina da shakara 7 aka sanya ni makarantar Elemantare ta Kayalwa wato acikin shekara ta 1947 zuwa 1951. Na samu damar tsallakawa zuwa makarantar midil har ila yau dake cikin garin na Katsina acikin shekara ta 1952 zuwa 1953. A shekara ta 1954 naje Kwalejin Barewa dake Zariya har zuwa shekarar 1959. Bayan na gama Kwalejin Barewa sai kuma na shiga Cibiyar aikin fasaha dake Kaduna a shekara ta 1960-61. A taikace,na shiga kwasa-kwasai na share fagen shiga jami’a inda Allah yasa ina daya daga cikin daliban farko 162 da jami’ar Ahmadu Bello ta fara dauka acikin shekara ta 1962 kuma na farkon yaye a 1965 inda na samu digirina na farko akan fannin mulkin jama’a(B. A Public Administration).

Aminiya – Bayan kammala wannan karatu,shin an cigaba da wani ko wani abin aka tunkara?

Alhaji Isa Katsina – To a wancan lokaci ba kamar irin wannan lokacin bane,fita ta daga jami’a ke da wuya sai kawai Gwamnatin jahar Arewa ta wancan lokacin ta dauke ni aiki a matsayin Babban Mataimakin Jami’in mulki(Assistant Secretary) a ma’aikatar yada labarai da fadakar da al’umma.

Aminiya – Kai tsaye aka dauke ka aikin ba tare da fuskantar matsala ba?

Alhaji Isa Katsina – To bari kaji inma baka labarin wani abinda ba zan mance da shi ba a lokacin da aka kira domin ganawa da ni(interview) daga su manyan hukumar daukar ma’aikatan(Civil Service Commission) wadda ake kira a takaice da ‘CSC’. A lokacin Marigayi Alhaji Abubakar Imam shi ya jagoranci wannan zaman ganawa. Tambayar da yayi mani ita ce, ‘me yasa kake son shiga aikin mulki bayan kuma ga ka da alamun kokari a wajen fannin da ya shafi kimiya,irin Physics da Chemistry?’. Amsar da na bashi ita ce,na fi son aikin da zai kusantar da ni ga jama’a domin samun saukin fahimtar halayensu da matsalolinsu ta yadda haka ne zan samu saukin gano hanyoyin da zan taimaka masu wajen kawo canje-canje na alheri a rayuwarsu, a matsayina na ma’aikaci. Kuma fara fahimtar hakan tun ina Barewa a lokacin da na rike mukamin Mai Unguwa(House Captain) na “Mort House” acikin shekarar karatuna na karshe a makarantar, 1959.

Tashin farko,sai aka kai ni ofishin Firimiya Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato(Allah ya jikansa da rahama) a matsayin Mataimakin Sakatare a fannin shari’a a ma’aikatar kananan hukumomi a wannan shekara ta 1965 wadda kuma ita ce shekarar farko da na fara aiki a matsayin jami’in gwamnati. Na kuma samu canjin wajen aiki a tsakanin shekara ta 1966/7-1968 zuwa hedkwatar Kabba ta Lokoja a matsayin Di’o mai kula da En-e En-e guda uku dake cikin Lokojar kuma a wannan lokacin ne ita Lokojar ta rika shan lugudan wuta daga Ojukwu saboda yakin Biafra. A 1968-70 na zauna a Zariya a matsayin Babban Di’o(SDO) mai kula da Kabba,Ijumu da Bunu(BIK) da Yagba ta Gabas da Yagba ta Yamma. Har’ila yau, ina bisa wannan mukamin ne aka kirkiro sabbin jihohi a Najeriya a shekara ta 1968 tare da kirkiro jahar Arewa ta Tsakiya wadda aka ajiye Hedkwatarta a Kaduna.

Aminiya – To duk wannan juya-juyar da ake yi da kai baka taba kawowa kanka damuwa ba?

Alhaji Isa Katsina – Damuwar me? Aiki ne fa na gwamnati wanda saida ka rantse zaka yi kuma a duk inda aka kaika. Kuma a wancan lokacin ai ma’aikaci so yake a rika kai wurare daban-daban domin ya kara samun ilmi da kuma kara fahimtar zamantakewa a tsakaninsa da jama’a. Kuma kada ka manta a wancan lokacin yadda matsayin ma’aikacin gwamnati yake ga al’umma ta irin yadda ake girmama shi. Yanzu ne dai abubuwa duk suka canja. Wani abinma in kaga ana yi a aikin sai kaji kamar kayi kuka saboda lalacewarsa.

Aminiya – To bayan samun jahar Arewa ta Tsakiya, ina aka dosa?

Alhaji Isa Katsina – To, a takaice dai likkafa tayi ta yin gaba har Allah yasa na zama Sakataren Hukumar daukar Ma’aikata(CSC), kai ta kai har aka turo ni gida Katsina a matsayin Babban Sakatare mai cikakken iko(Divisional Secretary,Special Duties)daga 1976-79. To a wannan zaman ne na kafa Karamar Hukumar Katsina(Katsina Local Government), kazalika, a wannan lokacin ne na kafa wannan Unguwa da ake kira “Kofar Kaura New Layout” wadda yanzu wajen ya zama babban gari ba Unguwa ba. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya har lokacin da nayi hijra na koma Hukumar Kasa ta Cinikin Auduga(Nigerian Cotton Board)

Aminiya – Duk acikin canjin aikin ne ya kai ka can?

Alhaji Isa Katsina – A’a. Matsin lambar ‘yan siyasar dake mulki a wannan lokaci ya sanya na canja sheka(1979-1983). Kasan har akwai wannan’ yar matsalar tsakanin masu mulki na siyasa da kuma ma’aikatan gwamnati.

Aminiya – Kenan ya nuna ka koma gefe daya sai ido?

Alhaji Isa Katsina – Ina? Ai zaben da akayi wanda Alhaji Lawal Kaita ya zama Gwamnan jahar ta Kaduna,sai ya dauko ni daga can Funtuwa zuwa Kadunar ya kuma bani Shugaban Ma’aikata na jahar. Kasan basu dade bisa wannan mulki ba sojoji suka yi masu juyin mulki acikin 1984 su kuma sun shigo a 1983. Zowar Gwamnan Soja a jahar, Kwamandan Mayakan Sama Usman Ma’azu,maimakon in samu canjin wajen aiki kamar yadda nayi zato da farko ai kawai sai ya kara mani nauyin bisa wancan. Sai na zamo nine Sakataren Gwamnatin jaha kuma nine Shugaban Ma’aikatan jahar duk a lokaci guda wanda nadin ya fara aiki daga 1 ga Janairun 1984. Ina tare da Usman Ma’azu har kuma aka kawo Kanar Abubakar Dangiwa Umar acikin 1985. Na ajiye aiki a lokacin shi Dangiwa Umar a shekarar 1986 kamar yadda tsarin mulkin ma’aikatan gwamnati ya tanada.

Aminiya – Ko akwai wani abinda zaka iya tunawa a lokacin zamanka da shi Lawal Kaita?

Alhaji Isa Katsina – To duk da dai shekara daya suka yi akan mulki ba zance ba’a samu damar aiwatar da wani abu ba. Duk da cewa,ni ke shugaban ma’aikata na jahar yayin da wani shi Gwamna Lawal Kaita ya baiwa wani dan lardin Zariya daga bangaren kudu bai hanani dagewa ba na ganin an aiwatar da adalci ga kowane bangare. A lokacin hawansa mulki ya taras ana aiwatar da wani tsari ne a wajen rabo duk wani abinda ya shafi cigaban jahar ta Kaduna a tsakanin wadannan larduna biyu wato lardin Katsina da na Zariya. A baya ana kasa koma menene gida uku(kamar yadda gwamnatin da ya karba daga wajenta take yi)ana ba kudancin lardin Zariya da suka hada da su Kafancan da Zangon Kataf, sai kuma arewacin lardin na Zariya wato daga Kaduna zuwa karshen lardin cikin kasar Hausa, yayinda za’a ba lardin Katsina wanda ya hada tun daga bangaren Funtuwa da Daura da ita kanta Katsinar. Wannan tsarin ne shi Gwamna Lawal Kaita ya kawo gyara akansa na cewa lallai kashi biyu za’ayi kowane lardi ya dauki daya. Anan ne Zagezagi suka ce basu yarda ba. To na taka muhimmiyar rawa wajen ganin cewa wancan tsari na Lawal Kaita ya kai ga gaci. Abinda su Zagezagi basu yi la’akari da shi ba shine,duk da kudancin Zariyan akwai kabilu daban daban yayin da lardin Katsinar baki dayansa Hausawa, amma kuma lardin yafi kudanci da arewacin lardin Zariyar yawan jama’a. Domin a wancan lokacin daga Kaduna sai Zariya sai kuma ita Kafancan ke manyan garuruwa. To har gobe ina alfahari da wannan domin ya kara kawo mani amincewa a tsakanin bangarorin biyu ta irin yadda suka ga ina da rikon gaskiya da kuma son ayi adalci.

See also  Buhari to commission projects in Kaduna

Aminiya – To zaman hutawa aka cigaba da yi bayan ajiye aikin?

Alhaji Isa Katsina – A’a. Ban zauna haka nan ba domin Bankin Cinikayya da Masana’antu na Najeriya(NBCI) ya dauke ni a matsayin shugaba, wato aikin jeka-ka-dawo har zuwa 1989. Daga nan kuma sai Marigayi Janar Shehu Musa ‘Yar’ aduwa ya bani Manajan Kamfaninsa na yin Darduma mai suna ‘Hamada Carpets dake nan ciki  garin Katsina har zuwa 1995. Kazalika,na sake komawa Babban Sakataren Gwamnatin jahar Katsina a 1999 lokacin da Marigayi Umaru Musa’ Yar’aduwa ya zama Gwamna. Na rike masa wannan kujera tun daga 2000 har zuwa 2003.

Aminiya – Shin bayan aiki tare da Sardauna, ko akwai wasu manya misali sarakuna da kayi aiki da su?

Alhaji Isa Katsina – Akwai bakin gwargwadon wadanda zan iya tunawa. Bari in fara da gida. Nayi aiki tare da Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo,Sarkin Daura Mamman Bashar,Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu,Sarkin birnin Gwari Jibrin Maigwari,sarkin Kagoro Gwamna Awan, Etsu Nupe Alhaji Usman Sarki da Umaru Sanda Nyako, su sarkin Dass Bilyaminu. Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Saddik III da sauransu. Hatta a jamhuriyar Nijar, irinsu sarkin Gobir na Tsibiri Agada Nagoggo, sarkin Dosso Alhaji Adamu Djermakoi, sarkin Katsinar Maradi da sarkin musulmi na Damagaram har su biyu. Kusan mafi yawan daga cikin irin sarakunan da nayi aiki da su duk Allah ya karbi abinsa.

Aminiya – Har yanzu banji kayi maganar karin neman ilmi ba.

Alhaji Isa Katsina – Lallai anyi irin wadannan tafiye-tafiye na neman karin ilmi ciki da wajen kasa, kai harma da na bude ido. Ban manta zuwa na Kwas a kasar Yugoslavia acikin shekarar 1971 domin ta bani damar saduwa da tsohon shugaban yakin Duniyar nan da ake kira Marshall Josip Broz Tito domin har liyafar cin abinci da shi ya shirya mana ni da abokan kwas dina. Har ilau, a dai cikin wannan shekara naje kasar Holland(Netherlands) nan ma na hadu da Sarauniyar kasar Marie Wilhelmina, nan ma a Amsterdam ta shirya mana liyafar cin abinci. Wadannan na kadan daga cikin kasashen da naje da kuma irin abinda aka yi mani wanda ba zan manta da shi ba

Aminiya – Hakika,duk wanda ya aiwatar da irin wannan aiki ba zai rasa samun takardar yabo ba.

Alhaji Isa Katsina – (murmushi). Bama takarda ba har lambobin yabo na samu. Kaga na samu O. F. R(Order of the Federal Republic)wadda Marigayi Sani Abacha ya bani a 1997. Sai Shugaban kasa Obasanjo(yana mulkin farar hula) ya bani C. O. N(Commander of the Order of the Niger). Wannan daga bangaren Gwamnati kenan. Su ma ‘yan boko,’yan kasuwa da’yan siyasa da sarakuna duk sun bani takardun shaidar karramawa.

Aminiya – Ko akwai wani bambancin aikin da dana yanzu?

Alhaji Isa Katsina – Kwarai da gaske! Dauki misali,hangen na sama da ma’aikata ke yi shi ya jaza aikin gwamnati yanzu ya lalace. Sabanin da wanda kokari da hazakar mutun ke sanyawa a ciyar da shi ba amma a yanzu ba haka abin yake ba. A yanzu neman mukami na gaba koda kuwa ba’a cancanta ba shi ma’aikatan wannan lokacin suka sa gaba. A yanzu ma’aikaci zaiyi amfani da kudi domin ganin ya matsa zuwa ga wancan ofis. Kuma zaiyi kokarin kafa wata ‘yar kungiyar mutane wadanda zai rika basu kudi domin kare muradunsa da kuma waccan bukatar da yake da ita. Ga karancin da’a, ba abin doka da oda ta aiki. Ma’ aikaci dole ya bi abinda na samansa ke so ba dokar aiki ba, in kuma har ba zai bi ba to saidai ya ajiye aikin. Ada in ance kaine shugaba a wuri,to hatta da kudaden da za’a gudanar da aiyukan inda kake jagoranci. Kuma saboda tsananin kiyayewa da tabbatar da ka rike amanar da aka baka,doka dan tumbin ciki akaga ka fara yi ko kuma wata shigar da ta wuce karfinka yanzu kaga masu bincike sunzo maka domin jin yadda akayi,amma yanzu dubi abinda ke faruwa. Ga rashin cika alkawali,domin alkawalin da ka dauka shine, zaka zo aiki lokaci kaza zaka kuma tashi lokaci kaza,ana yin wannan a yanzu? Maganar girmama na gaba duk ta kaura. Abubuwa ga su nan muna gani.

Aminiya – To menene shawararka ko mafitar abin?

Alhaji Isa Katsina – To indai maganar gyara zaka yi sai ka fara tambayar su wa zasu yi gyaran? In kace matasa masu tasowa a yanzu sai ince,to yaya zaka yi da son kudin da suke da shi? Ina maganar shaye-shayen da suke yi? Wato abin yana neman nazari tare da dauki. Ni a nawa tunanin, maganar gyaran aikin gwamnati da ma kowane irin aiki da kullum ake yi abin ba zai samu ba sai ni da kai mun shigo ciki mun bayar da tamu gudunmuwar. Abinda nike nufi anan shine, sai an shigo da tsaffin ma’aikata da kuma wadanda suka gogu akan aiki domin nuna yadda ya kamata a tafiyar da aikin. Amma yanzu sai kaga an dauki mutun aiki yau, gobe sai ace shine shugaban bangare kaza ba kuma tare da yasan wani abu a sashen ba kawai shike nan an cigaba a haka. A karshe babbar shawarata ita ce,a rike gaskiya da amana a kuma kiyaye cika alkawali tare da bin doka da oda. Nagode

 

 

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here