A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a yau Talata a Abuja, Ministan Watsa Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammed, ya kuma kalubalanci PDP da ta nuna lallai afuwar da take nema ta gaske ce ta hanyar sauya halayyarta na dawo da kudaden da aka sace lokacin mulkin jam’iyyar.
Gwamnatin ta fitar da sanarwar ne a matsayin mayar da martani kan wata sanarwa da tun da fari jam’iyyar PDP ta fitar, inda take neman afuwan ‘yan kasar game da kura-kuran da ta tafka a lokacin da ta mulki kasar na tsawon shekara 16.