Daga Jamil Adamu Balarabe
‘Dan majalisa Dipo Olorunrinu mai wakiltar mazabar Amuwo-Odofin ta jihar Legas daga jam’iyyar PDP ya bukaci jam’iyyarsa ta PDP da ta tsaida tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar don takarar kujerar shugaban Kasar Nijeriya.
Olorunrinu, ne kadai dan majalisar dokoki jihar Legas daga jam’iyyar PDP wanda ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na (NAN) yau Laraba a Legas.