BITA DA KULLIN BINCIKE: WANE ‘’ LAIFI’’HUKUMAR SUFURIN [KTSTA] TA JAHAR KATSINA TAYI?

0

Daga Danjuma Katsina

Hukumar sufuri ta jahar Katsina ,wadda aka fi sani da KTSTA na daga cikin hukumar sufuri da tayi tasiri da suna da kuma samar wa masu karamin karfi da mabukata hanyar safara a kasar nan, a baya ta zama abin misali da kuma wasu jihohi suyi takakkiya har jahar Katsina domin daukar darasi akan yadda hukumar ta zama murucin kan dutse.

Hukumar an kafa ta a shekarar 1992 lokacin mulkin farar hula da soja zamanin Alhaji saidu barda yana gwamnan Katsina. Na farar hula na farko A lokacin Alhaji Aminu bello masari [ gwamnan Katsina a yanzu] yana kwamishinan ayyuka na jahar Katsina.
Tun daga kafa ta take bunkasa da habaka da cigaba sai a wannan gwamnatin ta APC da lamarinta yake ci baya har tana gab da durkushewa. Tana shirin shiga kundin tarihin cewa ada ta taba bunkasa. Yanzu kuma tana ci baya.

Muhimmacin hukumar da kuma irin gudummuwar da take bayarwa ya sanya a baya gwamnati na tura mutum mai muhimmaci a wajensu ne.kuma su bashi goyon baya. A baya daga cikin wadanda suka rike hukumar kuma suka taka rawar gani da taimakon da suka samu a wajen gwamnatin jaha . sune dakta Mustafa inuwa sakataren gwamnatin jahar Katsina a yanzu. Da Malam Hadi sirika ministan jiragen sama a najeriya,da dakta bishir gambo saulawa. Da alhaji gambo rimi da sirajo aminu makera.

Hukumar na daya daga cikin abin da dan Katsina kan amfana kai tsaye daga wani aikin rangwame na gwamnatin jahar Katsina. Tana samar da motoci masu tafiya bangarorin kasar nan a cikin rahusa da lamuni,ga kuma tsaro da tuki daga kwararrrun direbobi masu da a da ladabi saboda horon da suka samu daga hukumar.

Hatta masu galihu daga wasu jihohin in har suna son ajiye motocinsu sun gwammace su shigo motoacin hukumar da su shiga wadansu motocin. Don haka kana iya cewa hukumar na amfanan kowa a jahar ba wai masu karamin karfi ba.

Duk wannan tasiri da suna da suka yi yanzu yana gab da zama tarihi, domin kullum hukumar baya take kara ci tana kara durkushewa kamar yadda bincike nay a tabbatar mani.motocin sun tsufa babu kayan gyara sai dosa na .babu abinda ke tabbas a hukumar a yanzu.

ME YE MATSALAR?
Bincike na ya tabbatar mani cewa gwamnatocin baya suna tallafawa hukumar akai akai da kudin sawo sabbi motoci da gyaran wadanda zasu gyaru da kuma duk wani karfin gwaiwar da hukumar ke bukata.. kamar yadda na tattauna da wasu da suka taba jagorancin hukumar suka tabbatar mani. Bakin su yazo daya da murya daya kamar haka.
‘’ lokacin da muna shugabanci gwamnati akai akai na duba bukatunmu kuma su biya mana..wannan yasa hukumar ke rike kanta da kanta ita ke daukar nauyin albashin duk mai aikatanta da kuma gudanarwarta har ma akai akai mu rika sayen sabbin motoci da fadada wasu ayyukan hukumar’’

Wannan a jumlace Magana daya da duk tsaffin shugabannin hukumar suka tabbatar mani..illa kawai kowane shugaba da salon yadda ya tunkari matsalar da ya iske da kuma tsarin yadda yabi ya kawo tasa nasarar kafin ya bar wajen
Bincike nay a tabbatar mani da cewa tunda wannan gwamnatin ta APC ta hau bata baiwa hukumar ko taro ba. Kamar yadda bincike a dukkanin hukumomin kudi ya tabbatar mani.duk kuwa da cewa lokacin da gwamnatin ta shigo komai ya kara farashi kusan kashi dari cikin dari.

Wata takarda da na gani wadda hukumar ta rubutawa gwamnan Katsina tana neman a bata wasu kudi don su gyara motocinsu su kuma tada komadar hukumar .bukatar da bata samu shiga ba. kuma a dai dai lokacin ga motocin suna gab da tsayawa.

Don haka jami an hukumar basu da mafita dole suka ciwo bashi a wajen wasu attajiran Katsina guda biyu,sune Alhaji Dahiru bara u mangal da Alhaji Abdul aziz maigoro da kudin bashin ne suka iya tada wadansu motocin suka farfado da ayyukan hukumar gadan gadan na wani dan lokaci da yanzu sun koma gidan jiya. Kamar yadda bincike na ya tabbatar mani.
Bincike na ya gano cewa da jami an hukumar suka kara tuni ga gwamnatin jaha cewa hukumar fa zata durkushe in ba a kawo masu dauki ba. maimakon su samu tallafi sai aka umurchi odita janar na jaha da binciki hukumar.

Binciken da na yi a ofishin odita janar ya tabbatar mani da suna binciken hukumar wani da nayi Magana dashi bisa amana yace ‘’ mun tattaro duk takardunsu da littafansu sama da sati hudu kenan amma gaskiyar Magana har yanzu bamu ga komai ba..inajin shugaban ko hukumar na da wata tsama da gwamnatin ko wani cikin gwamnatin kona kusa da gwamna’’
Binciken da na yi akwai wasu bangarorin gwamnati ‘’ yan lele’’ wadanda ake sakarwa kudi ba tare da bin kadin me suke da kudinsu ba.kuma ba a bincike su ba. misali hukumar wassanni ta jaha wadda filin wasan karkanda ke hannunsu.

Suna samun kudin shiga masu yawa amma duk da haka gwamnati na tallafa masu. Akai akai. Ko kwanan nan an majalisar zartarwar jahar ta amince da bada kwangilar sama da naira milyan dari biyu na inganta filin wasan.

Binciken mu ya kuma gano yadda gwamnatin jahar ke daukar nauyin wani da ta mallaka ma filin shakatawa na Maryam park dake kallon massalacin banu coomassie. Dake unguwar masu galihu ta jahar Katsina,Ga wani da ya ce zai kawo ma jahar kudin shiga in aka mallaka masa wajen.ana zargin an bashi wasu kudin tallafin da zai gudanar da wajen,amma tabbas marubucin nan yaga wasu takardu da suka shafi kudin abincinsa da kwana hotal wanda kudin sun haura ma miliyan talatin wanda gwamnati ta dau nauyinsa,Amma har zuwa rubuta labarin ko kwabo bai shigarwaa da gwamnatin jaha ba.

kuma abinda yake bai da wata alaka da tallakan jahar Tambayar da kowa keyi shine wane laifi hukumar sufurin tayi ba a tallafa mata ba. tana kakarin mutuwa aka kuma bita da bita da kullin bincike? Duk wani kokarin jin ta bakin hukumar yaci tura ganinsu ya wahalta shugaban kuma yaki amsar waya ta ko sakon kar ta kwana da na aika masa.

SANARWA.
Wannan sharhin an buga shi a jaridun leadership Hausa…Al. Mizan..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here