Ba Bu Wanda Ya Isa Ya Hana Ni Fadar Gaskiya – Dino

0

Daga Jamil Adamu Balarabe

Dan Majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Dino Melaye ya ce ba zai yi shiru da bakinsa ba matukar ya ga wani abu da ake gudanarwa a gwamnatin Buhari da bai dace ba.

Sanatan ya bayyana wa manema labarai cewa baya tsoron tsage gaskiya a duk inda ta kama a fade ta, ba kuma ya duba daga jam’iyyar da mutum ya fito indai batun gaskiyar ya kama ko dan jam’iyyar adawa ta PDP ne, ko kuma APC mai mulki.

Dino ya kara da cewa,  ‘Ni ba na tsoron kowa, idan akkai abin da ba daidai ba kuma na ga babu gaskiya a ciki sai na fada, ba na jin tsoron kowa indai ina da gaskiya,’ inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here