Fadar Mai Marba Sarkin Katsina Ta Yi Cikar Dango

0

Daga Abdulrahman

A jiya juma’a ne  30 ga Maris 2018 Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya halarci nade-naden sarauta da mai martaba Sarkin Katsina ya yi wa wasu fitattun Mutane a Jihar nan.

Daga cikin wadanda aka nada din akwai, Kakakin Majalissar Dokokin ta Jihar Katsina Alhaji Abubakar Yahaya Kusada wanda aka nada a matsayin Garkuwan Katsina da kuma tsohon mataimakin gwamnan Jihar Katsina Alhaji Abdullahi Garba Faskari a matsayin Danyabanin Katsina da Shugaban Kwalejin Illimi ta gwamnatin Tarayya dake Katsina Dakta Aliyu Idris Funtuwa a matsayin Garkuwan Malaman Katsina, tare da Dan majalissar Tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina Hon Sani Aliyu Danlami a matsayin Garkuwan Arewan Katsina, da sauran wasu sarautu da dama.

Wannan gagarumin biki ya samu halartar mutane daga sassa da dama na kasar nan wadanda suka hada da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu da Hon Alasan Doguwa dan Majalissar Tarayya daga Kano wanda ya wakilci Kakakin Majalissar Dokoki ta kasa, da Shugaban bankin samar da gidaje na Tarayya Alhaji Ahmed Musa Dangiwa, da sauran mutane da dama.

Fadar ta yi cikar da aka dade ba a ga irinta ba, musamman yadda wadanda aka nada din suka zo da gayyarsu ta yan uwa da abokan arzuka. An yi dai nadin lami lafiya cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Sannan an yi jawabai da dama kan dacewar wadanda aka nada din.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here