Jami’an ‘Yansanda Sun Bayyana Wa ‘Yan Jarida Nasarorin Da Suka Samu

0

Daga Bishir Suleiman S/Kasuwa

A ranar laraba ne, rundunar ‘Yansandan jihar kwara ta tasa ƙƴeyar waɗanda ake zargi da aikata laifukan tsafi. An kama matsafin da ƙoƙunan kan mutane a garin Ilorin. Kwamishinan ‘Ƴansanda Lawal Ado ya bayyana cewa an cafke Sulaiman Adenifuja da ƙoƙunan kan mutane guda uku a kan hanyar Ogbomosho a yankin Eiyekorin dake ilori a ranar 26 ga watan maris na shekarar nan.
Kwamishinan ya ƙara da cewa binciken da suka gudanar ya nuna wanda ake zargin yana safarar ƙoƙunan ne tsakanin jihar Legas da Ilorin ta jihar Kwara, domin gudanar ayyukan tsafi.

Haka kuma rundunar ta bayyana kamun Wahab Romoni wanda ake zargi da satar mota kirar Toyota Camry mai lamba AKD 287 EE wanda tuni aka halarta ta hannun mai mallakinta na aihini bayan kammala bincike, an kuma tisa ƙyeƴar wanda ake zargi a gaban koliya.

Kazalika, Kwamishinan ya gargaɗi mazauna yanki da su guji sanya amsa kara tsaye ba tare da ƙa’ida ba, da kuma ɓoƴe lambabin mota ba bisa ƙa’ida ba, musamman ma ga motocin Bankuna dana wasu hukumomi. Ya ƙara da cewa in har za a yi haka sai an samu takardar amincewa daga Sufeton ‘Ƴansada na Ƙasa Ibrahim K Idris a rubuce. Ya ƙara da cewa rundunar a shirye take ta damke duk wanda saɓa wannan umarni tare da tisa ƙyeyarsa zuwa gaban shari’ah.

Kwamishinan ‘Yansadan ya kuma sanar cewa za a janye jami’an ‘ƴansanda  da ke aiki a tare da ‘ƴansiyasa da wasu jami’an Gwamnati daga nan zuwa 20 ga watan Afrilu, amma dukkan wanda abin ya shafa na iya neman a ƙara bashi jami’in ta tsaro ta hanyar rubuta takarda ga Sufeton ‘Ƴansada na ƙasar nan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here