SINADARIN DASA KAUNA

0
2167

Abdurrahaman Aliyu 08036954354

Akwai wasu abubuwa da dama masu tasiri a cikin lamuran soyayya,amma ma fi yawan lokuta akan samu cewa ‘yan mata ba su fiye bada hankalin su a wannan wajen ba,sukan manta da irin wadannan abubuwansu fake da cewaa ai lallai namiji shi ne mai kashe da rabawa,shi ne ya kamata ya yiwa mace komai,amma ni a hangena sai na ke ganin akwai bukatar ayi nazari a yi duba akan hakan.Ya kamata ko waccce budurwa ta san da wadannan ni nawa ra’yin ke nan.

1-Nuna Damuwa

Akwai bukatar mace ta dinga nunawa saurayi ta damu dashi,duk lokacin da ta kwana biyu bata ganshi ba ta tuntube shi taji ko lafiya,za ta iya hakan a wannan lokaci idan yana da waya ta kirasa,ko ta aiki wani kanin ta ya binciko mata a gidan su, ko ta yi masa sako, ta dai nuna masa ta damu dashi.

 

2-Fahimtar Halaye

Budurwa ya kamata ta san halayen saurayin ta, mai yawan bacin rai ne, wato saurin fushi, ko kuma mai saukin kaine, shin yana bukatar tayi abu kaza, ko baya so, shin wane irin yanayi yake so ya ganta? Cikin nutsuwa kullum, ko ko cikin raha da nu na annushuwa, wane abu ne ya fi so a rayuwarsa wanda yafi birgeshi,musamman lokacin da suke tare, mai budurwa za tayi masa yafi jin dadi, idan yayi fushi mai yakamata tayi masa su wanye lafiya ta dawo masa da farincikin sa.

 

3-Son Abin Da Yake So

Budurwa ta dinga nunawa saurayin ta son abun da yake so, ta lura duk abun da yake so indai ba wai ya saba da halayyar dan adam ba, wato ta fannin addini ko sabawa al’ada ta wannan al’umma, ya kamta su yi tarayya  a kan abun da yake so (bawai ina nufin dole ra’ayin su ya zamto daya ba, za su iya sabawaa wajen nuna ra’ayi).

4-Gujewa abin da baya so. Ya kamata ta gujewa duk wani abu da tasan idan tayi zai bata masa rai.

5-Nuna Masa Kauna

Akwai bukatar mace ta dinga nuna wa saurayin ta kauna a zahiri, ban yarda da boye kauna ba, wannan rashin yarda ne indai an amince da juna, amma mace za ta dinga nuna kunya wani lokacin, wannan kuma kamar gishirine a cikin miya. amma ya kamata a nuna kauanar a zahiri, ba wani boye boye.

6-Kyautata masa

 

Tabbas zuciya an gina ta a kan son wanda yake kyautata mata da kin wanda yake muna na mata, akwai bukatar budurwa ta fahimci cewa namiji ma yana son mace tayi masa kyauta, kamar yadda mata suke sa ran namiji zai yi musu kyauta, Budurwa ya kamata ta dinga bawa saurayin ta kyauta wato kyauta ba wai sai mai yawa ba, a a kamar ta sayo biro mai kyau, ko ta sayo masa chacolate, ko ta sayo masa wani littafi na karantawa, musamman idan makaranci ne, hakazalika akwai bukatar ta dinga kyautata masa duk lokacin da yazo wajen ta, wannan zai kara daukaka ta a zuciyar sa, ya dinga ji da ita yana mai alfahari da ita, bawai saurayi ba, wannan ko ga mace ta aure, idan mijin ta ya fita aiki, ya bata kudin cefane ko ya sayo, amma watakila shi a nasa cefanen ba nama, ita kuma ta samu dan kudi, sai ta sayo nama, ta karo da vegetables da spices, ta hada masa wani drink mai dan a karan zaki, habaaaaaaa, ai kawai wannan sai dai a tamabayi angwaye na kwanan nan.

7-San cigaban sa

Yi masa addu’a a kowane lokaci, da son cigabansa a rayuwa, da rashin nuna masa gazawa.saboda ba kowane lokaci bane zaka samu mutum yana da kudi, amma an san lokacin da yake da samu yakan yi iayakar kokarinsa. To ina gad a mata zasu rike wannan da an samu saukin abinda ake kira yaudara.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here