Ta Shayar Da Mahaifinta Ruwan Nononta Don Kar Ya Mutu

0

Daga Abdulrahman Aliyu

“Da zaran ka kalli wannan hoton dake sama abubuwa da yawa ne zasu zo a zuciyarka, amma da zaran ka san hakikanin labarin sai ka zubda Kwalla a idonka”

A daya daga cikin kasashen Turawa ne aka yankewa wani tsoho hukuncin kisa ta hanyar yunwa, in da aka tsare shi a gidan yari da niyyar ba za a bashi abinci ba har sai yunwa ta kashe shi.

Sai dai Diyarsa daya da ya mallaka a Duniya ta yi yarjejeniya da hukuma a kan kullum zata rika zuwa ta gana da shi har ya mutu.

Sai dai an umurci jami’an gidan yari da kar su barta ta shiga da wani abu da za a iya ci ko sha.

Bayan da ta lura da matsanancin halin da mahaifin nata ke ciki sai ta yanke shawarar shayar da shi ruwan nononta domin ya rayu, kullum in ta zo sai ta bashi nono ya sha.
Bayan daukar tsawon lokaci aka lura wannan mutum ya ki mutuwa, sai aka sa bincike har aka gano cewa wannan diyar ta sa ita ke shayar da shi ruwan nono. Aka kamata aka tuhumeta da laifin saba doka, amma saboda irin juriya da diyauci da ta nuna shi ya sauya ra’ayin alkalan suka sallami mahaifin nata, ya samu yancin walwala.

Diya mace ta na dauke da zuciyar sadaukarwa da jajircewa wajen ganin ta zama uwa ko ‘yar’uwa ko mata ta gari ta fuskar nuna tausayi da kyawawar niyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here