Ina Kayan Mazabarmu?

0

Dawa kayi shawarar ayyukan da mazabar Dutsin-Ma/Kurfi Ke Bukata?

Zuwa ga Hon. Danlami Kurfi.

Kwanan nan nasamu wasu takardun daga hukumar BudgeIT na ayyukan da yanmajalissu suka nema ayiwa mazabarsu tun daga shekarar 2015 zuwa 2017. A cikin ayyukan da ka nema sun hada da:

1) Samarwa  mazabar Dutsin-Ma/ Kurfi mashina na Miliyan Hamsin (50,000,000)
2) Abaka Keke-Napepe na miliyan Ashirin da Biyar (25,000,000).
3) Ka amshi miliyan talatin (30,000,000) don tallafawa mata da matasa jari
4) Ka amshi miliyan goma (10,000,000) don gudanarda aikin koyawa matasa sana’u.
Shin Danlami, waya gaya maka Mashin da Napep ne matsalar mutanen mu?
Sanan suwa aka rabawa Mashina Har na Million N50,000,000? Napep na million N25,000,000?
Wasu yan majalissun har hanya, asibiti naga suna requesting ayi masu, kai me yasa kake requesting kayan kudin?
Inaso abani bayani dalla-dalla, kar kashin dokar freedom of information act!
Inason abani sunaye da addereshin mutanen da aka rabawa mashina, napep, Wanda kaba jari da wanda akaba horarwa ta sana’u.

Daga Dan-Mazabarka,
Ibrahim Bature.
Unguwar Dabino,
Dutsin-Ma A.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here