Daga Bishir Suleiman S/Kasuwa
Dukkan ‘yan majalissar dattawa guda uku da suka fito daga jihar Kaduna basu amince da ciwo wa jihar bashi ba.
Kamar yadda gidan talabijin na TVC ya ruwaito a Abuja ‘yan majalissar dattawan sun ki amincewa da buƙatar neman cin bashi da gwamnatin jihar Kaduna ta nema daga asusun Bankin Duniya.
Shugaban kwamitin bayar da lamuni cin bashi na cikin gida da ƙetare na majalissar dattawan sanata Shehu Sani a rehoton da ya gabatar wa wakillan majalissar a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnati jihar ba za tai abin da zai amfanar al’ummar jihar ba, da rancen wanda shi ne maƙasudin kin amincewarsa.
A nasa ɓangaren sanata Suleiman Huƙuyi da ke wakiltar Kaduna ta arewa ya ƙara da cewa sun ki ba takardar neman ciwo bashin kulawa ta musamman saboda za a ƙara wa jihar nauyin, sannan dalilan da jihar ta gabatar wa banki ya bambanta da abin da aka yi nufin yi da kuɗin.
Ya ci gaba da cewa za a yi amfani da kuɗaɗen ne don wasu buƙatoci na gwamnatin jihar.
Shi ma sanatan da ke wakiltar Kaduna ta kudu, sanata Ɗanjuma la’ah ya ki amincewa da takardar neman rance, inda ya ce jama’ar jihar ba su muradin sake ciwo ma su wani sabon bashi.
A ɓangare guda mataimakin shugaban majalissar dattawan sanata Ike Ekweremadu wanda ya yi magana a madadin shugaban majalissar, ya bayyana cewa takardar da gwamnatin ta gabatar na dalilan cin bashi na gina ƙasa ne, bai saɓa wa ƙa’ida ba, sai dai an samu rashin daidaito ta ɓangaren tuntubar wakilan jama’ar jihar, wanda yin hakan ya nuna ana wa damakaradiyya karen tsaye a jihar.
Da ya jefa tambayar amincewa ga sauran ‘ƴanmajalissar dattawan mafi yawancinsu sun ki amincewa da takardar ƙudurin ciwo wa jihar ta Kaduna bashin dala miliyan 350 da gwamnatin ta gabatarwa majalissar.