Na Shiga Aikin Shari’a Ne Domin In Yi Adalcin: Justice Musa Danladi Abubakar

0

Daga Abdulrahman Aliyu

A ranar Lahadi 1/04/2018 ne cibiyar Koyan Sana’o’i ta Marigayi MD Yusuf Karkashin Jagorancin fitaccen Danjarida Malam Danjuma Katsina tare da hadin guiwar wasu masoyan Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar suka shirya taron addu’a ga Maisahri’a domin yi masa fatan gamawa lafiya da samun nasara a bisa babban Matsayin da ya samu na zama Alkalin-Alkalai na Jihar Katsina.

Taron addu’ar ya samu halartar Malamai da ga sassa da dama cikin garin Katsina.
Sannan an yi jawabai masu ratsa zuciya kan rayuwa da ayyukan kwarai na Maishari’a Musa Danladi Abubakar.
Daga cikin wadanda suka yi jawabai akwai Tsohon Kakakin Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina Garkuwan Daura, Turakin Damagaram Alhaji Ya’u Umar Gwajojo, in da ya yi karin haske da cewa duk halin da muke ciki a kasar nan hadda rasa irin su Maishari’a da aka yi,  a takaice taimako ya yi karanci tsakanin mu, in da ya bada shawara kamata ya yi mu yi koyi da halin Maishari’a Na taimakon juna tsakanin mu.
Haka ma Shugaban Cibiyar ta MD Yusuf Malam Danjuma Katsina ya yi bayanin cewa tun da aka bude wannan jibiya Maishari’a ke taimaka mata, kuma a duk ranar juma’a sai sun yi mashi addu’a ta neman Allah ya ba shi Nasara a rayuwarsa.

See also  An daure matashi shekaru 40 a gidan gyaran hali, bayan ya tsere wata 4 kafin wa'adinsa

A bangaren Mata ma, Malam A’isha Mobile ta yi bayanin cewa Maishari’a ya dace mata na gari wadanda suke taimaka mashi wajen gudanar da ayyukan rayuwarshi, shi ya sa kullum Nasara ke bibiyarsa.

A nasa jawabin godiyar Maishari’a ya yi bayanin cewa shi mutum ne kamar kowa, irin hanyar da ya dauka ta taimakon al’umma kowa ma zai iya sadukarwa ce kawai da jajircewa, sannan ya yi bayanin cewa shi dama ya shiga aikin Shari’a ne domin ya yi Adalci, kuma ba wani matsayin koukami da zai iya sauya shi daga halin da aka san shi da shi ko da kuwa shugaban kasa ya zama.

An tashi taron bayan an rarraba abinci ga mahalarta taron addu’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here