PDP Ce Ta Talauta Kasar Nan

0

Daga Abdulrahman Aliyu

A Karo Na Biyu, Gwamnatin APC Ta Sake Fidda Sunayen Jiga-jigan PDP Da Suka Wawushe  Dukiyar Nijeriya.

Ministan yada labari da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce mutane ba su gane dalilin da ya sa ba su saki dukkan sunayen a karo a farko ba, cewa jerin farko somin tabi ne kawai.
A karo na biyu sun sake fito da sunayen da kuma kudaden da kowane daga cikin su ya hadiye.

Ga jerin sunayen nasu;

 1. Tsohon NSA Sambo Dasuki: $2.1bn, N126 billion, $1.5 billion, Fam 5.5 miliyan
  2. Tsohon ministan man fetur Diezani Alison-Madueke: N23bn, $3 billion
  3. Laftanal Janar Kenneth Minimah: N13.9 billion
  4. Laftana Janar Azubuike Iejirika: N4.5 billion
  5. Tsohon shugaban soji, Alex Barde: N8billion
  6. Tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde: N40 billion
  7. Air Marshal Adesola Amosun: N21.4 billion
  8. Tsohon ministan FCT, Sanata Bala Abdulkadir: N5 billion
  9. Sanata Stella Oduah: N9.8 billion
  10. Tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu: N1.6 billion
  11. Tsohon gwamnan jihar Flato, Jonah Jang: N12.5 billion
  12. Tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda: N1.5 billion, $829,800
  13. Sanata Peter Nwaboshi: N1.5billion
  14. Aliyu Usman: N512 million
  15. Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashid Ladoja: N500 million
  16. Tomi Ikimi: N300 million
  17. Femi Fani-Kayode: N866 million
  18.Hassan Tukur: $1.7 million
  19. Nenadi Usman N1.5 billion
  20. Benedicta Iroha: 1.7 Billion
  21. Aliyu Usman Jawaz: N882 million
See also  Babbar kotun Tarayya dake Kaduna ta yanke ma Hon Mansir Ali Mashi hukuncin shekaru biyar a gidan yari

Tun da farko dai gwamnatin tarayya ta saki jerin sunayen wasu manyan jigogin PDP da suka wawuri dukiyar Nijeriya
kamar haka;

1) Shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus: Ya karbi miliyan 200 ranar 19 ga watan Fabrairun 2015 daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro (NSA).

2) Tsohon sakataren kudin jam’iyyar PDP: A ranar 24 ga watan Oktoba, 2014, ya karbi miliyan N600m daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa a kan harkar tsaro.
3) Tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP, Olisah Metuh: Ana tuhumar sa da karbar biliyan N1.4bn daga ofishin tsohon NSA.
4) Dakta Raymond Dokpesi: Shugaban kamfanin DAAR; mai gidan talabijin na AIT da gidan Radiyon Ray Power. Ana tuhumar sa da karbar biliyan 2.1 daga ofishin tsohon NSA.
5) Tsohon mai bawa tsohon shugaban kasa Jonathan shawara, Dudafa Waripamo-Owei: An gurfanar da shi bisa boye kudi miliyan N830m a asusu daban-daban.
6) Robert Azibaola: Dan uwa ga Jonathan: An gurfanar da shi gaban kotu ranar Alhamis bisa tuhumar karbar Dala biliyan $40m.

Wadannan su ne jerin farko da gwamnatin APC ta fara saki kafin daga baya ta saki sauran.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here