…tun kafin na musulunta idan na ji an ambaci Annabi (S.A.W) sai na ji dadi a raina, cewarta
Daga Umar El-Farouk
Bayan shafe sama da shekaru dari 100 yanzu haka wata mata da aka yi ittifakin babu sa’anta a yankin Karshi dake Abuja Allah cikin ikon sa ta karbi musulunci, bayan shafe shekaru ana fama da ita musamman ‘ya’yanta da jikokin ta amman abin ya gagara, Allah cikin ikon sa sanadiyar Mauludin da aka shirya don auren wani jikanta daga nan Allah ya sa mata zuciyar musulunci.
Sheikh Adamu Inuwa shi ne Babban limamin garin Karshi FCT ya ce, akwai lokacin da ta tara ‘ya’yanta tace duk wanda ya kara cewa ta shiga musulunci sai ta yi Masa Baki, wannan yasa suke jin shakkar kiran ta zuwa musulunci, amman ni duk da haka ban gaji da zuwa wajanta ba don da’awah.
Wani abin mamaki ga ita wannan baiwar Allah duk sanda ake Mauludin Manzon Allah SAW ko mu Zahara sai ta fito, har ma tana fadin duk sanda ta ji an ambaci Manzon Allah SAW takan samu nutsuwa a zuciyar ta.
Yanzu haka dai ta karbi kalmar shahada a wajan Babban limamin garin Karshi FCT, an kuma sa mata suna Rahama kamar yadda ta ce ta fi son wannan suna.