A safiyar yau Laraba ne, iyalan Dan majalissar Dattawa mai wakiltar mazabar Daura a Jihar Katsina, Mustapha Bukar suka bayyana rasuwarsa.
Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa yana sanar da Al’umma rasuwar sanatan.
“Marigayin ya ba da gudunmuwa sosai yayin da ake tattauna muhimman babutuwa a zauren majalisar,” in ji shugaban.
Daga nan ne sai ya yi fatan Allah Ya jikansa da rahma.
Zuwa yanzu babu wani bayani da aka samu kan musabbabin rasuwar dan majalisa, wanda ya rasu yana da shekara 64.
Marigayin wanda injiniya ne, an haife shi ne a garin Daura a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 1954.
Allah ya jikansa da gafara