Me Ya Kai Fati Muhammad Wajen Gwamnan Katsina?

0

Daga Ahmad Muhammad

Shararriyar Yar fim din nan Mai suna Fati Muhammad ta je Katsina​ Domin ganawa da gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari..Yar wasan wadda yanzu itace Babbar jakadiyar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar Wanda yake neman tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam iyyar Adawa ta PDP…

Binciken Taskar labarai..ya tabbatar da cewa Yar fim din  ta kwashe kwanaki a wani otal din Katsina.kuma wani Mai taimakawa gwamna Yana dawainiya da ita. Wanda daga karshe ta samu ganin gwamnan .

Amma Babu Wanda ya San me ya Kai ta me kuma suka tattaunawa, Taskar labarai, ta bincika ta kuma tabbatar cewa ganawa bata ofis bace, shi yasa ba  a ga Fati din a ofis ba, Amma ganawa ce ta kashin Kai.

Zuwan na Fati Muhammad Katsina yafi alaka da siyasa bana wasan fim bane. Domin duk ‘Yan fim din Katsina Babu Wanda ya San ta shigo. kamar yadda bincike Taskar labarai ya tabbatar,
Wani Dan fim yace zirga zirgar Fati Muhammad yanzu tafi dangantaka da siyasa fiye da harkar fim
Kuma kwananan shafin ta na Facebook ya yi kaurin suna wajen sukar salon mulkin shugaba Buhari, wannan yasa ganinta a Katsina Don ganin Gwamnan zai ba kowa mamaki.

Mun Aikawa Fati sakon wayar Hannu har zuwa rubuta rahoton nan bata bada amsa ba wani jami’in gwamnatin Katsina yace shi bai san zancen ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here