An fitar da zakarun da za su Fafata a Gasar Labarai Ta Pleasant Library and Books Da Makarantar Malam Bambadiya

0

Daga Abdulrahman Aliyu

A jiya ne Farfesa Ibrahim Malumfashi ya sanar da fitar da jaddawalin sunaye wadanda za su fafata a. Fitar da na daya zuwa na uku a Gasar. Farfesa ya bayyana cewa.

“Kamar yadda aka sanar a ka kuma alkawurta, ga sakamakon gasar da ke kunshe da mutane 15 daga cikin 50 da alkalan gasar suka zaba a matsayin wadanda labaransu suka burge domin kasancewa wadanda za su fafata domin amsar kambin wannan gasa a watan YUNI na 2018 in Allah a kai mu, a wani dan kwarya-kwaryan biki da za a yi a birnin Katsina
Wannan jadawali ba yana nufin shi ne sakamako na karshe ba, a’a, wadanda suka samu kai wa zagaye na karshe ne, daga cikin su za a fitar da na 1 zuwa na 3 wadanda za a ba awalajar N55,000 ga na daya, N35,000 ga na biyu sai N25,000 ga na uku. Sauran wadanda suka yi na 3 zuwa 12 za a ba kowannen su tukwicin N12,500.

Kamar yadda aka shelanta za a kuma tace da tsara da kuma buga wadannan labaran da suka ci gasar su 15, a matsayin littafi, a kuma kaddamar da su da yardar Allah.
Ga zakarun gasar:
1 Na’ima Abdullahi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Zagon Kasa
2 Kabir Yusuf Fagge Daga Jihar Kano, Taken Labari Matalauciyar Rayuwa
3 Zakariya Haruna Daga Jihar Kano, Taken Labari Da Sandar Hannunka
4 Fadila H. Kurfi Daga Jihar Katsina, Taken Labari Rayuwar ‘Ya Mace
5 Abubakar Yusuf Mada Daga Jihar Zamfara, Taken Labari Sauyin Rayuwa
6 Hamza Dawaki Daga Jihar Kano, Taken Labari Katantanwa
7 Ibrahim Babangida Suraj Daga Jihar Katsina, Taken Labari Hangen Dala
8 Hassana Abdullahi Hunquyi Daga Jihar Kaduna, Taken Labari A Sasanta
9 Kabiru Shu’aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Ragguwar Dabara
10 Amina Sani Shu’aibu Daga Jihar Kano, Taken Labari Balaguron Talauci
11 Fatima Husaini Ladan Daga Jihar Katsina, Taken Labari Kowa Ya Bar Gida
12 Ashiru Dan Azumi Gwarzo Daga Jihar Kano, Taken Labari Jamhuriyar Matalauta
13 Usman Muhammad Alqasim Daga Jihar Katsina, Taken Labari Dangina
14 Jamila Muhammad Lawal Daga Jihar Kaduna, Taken Labari Tsananin Talauci
15 Zaharadeen Nasir Daga Jihar Kano, Taken Labari Salmakal

See also  Murtalan Jikin Naira 20: Cikar Shekaru 40 Da Rasuwarshi

Mun gode”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here