Daga Bishir Sulaiman
Ƙungiyar Haƙuri Jari Ne wadda ke a jahar katsina, ta sanya gasar wasan ƙwallon zungure (SNOOKER) wanda ta yi wa laƙabi da 4+4 Masari 2019.
An yi bikin buɗe gasar ne a ranar 10/3/2018 a ɗakin taro na cibiyar horar da sana’o’i dake filin samji katsina, wanda mai girma Gwamnan jihar katsina Alh. Aminu Bello Masari Matawallen Hausa Dallatun Katsina, ya umarci Kwamishinan wasani na jihar da ya zama wakilinsa a wurin bikin buɗe gasar.
A cigaba da gudanar da wasannin da ake yi a cibiyoyin daban daban na ƙwaryar katsina, wadda wasu magoya bayan tafiyar 4+4 ke ɗaukar nauyin kula da hidimar gasar a sassan, inda a yau jagoran dake ɗaukar nauyin gasar shugaban hukumar tsaftace muhalli ta jihar katsina. Alh. Isah Barda ya buɗe santar GRA wadda ke a farfajiyar sayar da abinci ta canis, bikin ya samu halartar duban jama’a, magoya bayan tafiyar Dallatu. Kazalika, zakarun dake fafata gasar sama da mutum 300 waɗanda aka zaɓo daga ɗaukacin runfunan zaɓe na mazaɓun karamar hukuɓar ta katsina sun halarci bikin.
Shugaban hukumar adana kuɗaɗe ta jahar Katsina Alh. Sani Lawal Madawaki wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda ke kula da sassan da aka tanada dan gudar da gasar shi ne ya zamo babban baƙo wajen bikin buɗe santar ta GRA.
Haka kuma, bikin ya samu halarcim wakilin kwamishinan wasanni na jaha tare da sauran manyan baki.
A ɓangare guda kuma bikin ya samu halarcin ‘yan wasan film irin su Suleiman Ɓosho da Hajiya Binta Ƙofar soro da sauran yan wasan.
Da yake tattauna da ma nema labarai, shugaban ƙungiyar Alh. Lawal Snooker ya yi jawabi inda ya jawo hankalin matasa da al’aummar jahar katsina gaba ɗaya da su sakawa ƙoƙarin wannan gwamnati ta Dallatu, ta hanyar ƙara zaben ta a karo na biyu, shi ma Ma’ajin jahar katsina, ya bayyana irin ƙoƙarin da wannan gwamnati ke yi ta kowane sashe tare da yaba wa ƙoƙarin wannan ƙungiya da ta assasa wannan gasar tare da ɗaukar alƙawarin cigaba da tallafawa wannan ƙungiya a kan ƙudurinta da tasa a gaba.
A nasa jawabin, mai ɗaukar nauyin gudanar da gasar Alh. Isah Barda ya yi godiya ƙwarai ga maharta taron tare da addu’ar Allah ya ba mairabo sa’a.
Sannan ya yi jinjina ga irin ƙoƙarin Gwamnatin Dallatu, da yadda ta ke taimakon al’ummar jahar nan. Ya ƙara da cewa wasan ƙwallon zungure wasa ne na saka nishaɗi da ƙulla zumunci, kuma wanda ya ke ƙara dankon zumunta, ya kuma yabawa ƙoƙarin wannan ƙungiya ta yadda ta zaƙulo ɗimbin jama’a domim gudanar da gasar da yadda suke ta ƙoƙarin wayar da kan al’umma wajen saka wa ƙoƙarin da gwamnati ke yi. A ƙarshe mai ɗaukar nauyin gasar ya yi fatan alheri ga kowa da kowa da addu’ar Allah ya maimaita mana 4+4 Masari 2019 a kuma yi wasa lafiya a gama.