Masari bai yi ganawar sirri da Fati Muham-mad ba – S. A. Sabo Musa

0

Daga http://katsinaposthausa.com

Mai taimakawa Gwamnan jihar Katsina akan harkokin maido da jihar kan turba madaidaiciya watau S. A. Restoration, Alhaji Sabo Musa ya karyata rahoton da wannan kafar ta buga na Taskar Labarai da ya ce Gwamnan ya yi ganawar sirri da fitacciyar tsohuwar jarumar fim din Hausa Fati Muhammad.

Alhaji Sabo Musa ya bayyana hakan ne a wata fira da yayi da wakilin wannan jaridar inda ya bayyana cewa tabbas ba kamshin gaskiya a cikin labarin. A. Restoration ya kuma kara da cewa tabbas jarumar ta zo Katsina amma shi ya gayyace ta saboda yana so tayi mashi wani aikin da ke da alaka da tallata kungiyar da yake shugabanta ta Masari Restoration Awareness Forum (MRAF).

See also  SHIMANKAR COMMUNITY IN PLATEAU STATE EMPOWERED WITH SOLAR POWERED ELECTRICITY!

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mun wallafa wani rahoton da Jaridar Taskar Labarai tayi inda ta bayyana cewa shararriyar yar fim din nan Mai suna Fati Muhammad ta je Katsina​ Domin ganawa da gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari.

Yar wasan wadda yanzu itace Babbar jakadiyar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar Wanda yake neman tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam iyyar Adawa ta PDP.

Binciken Taskar labarai ya tabbatar da cewa Yar fim din ta kwashe kwanaki a wani otal din Katsina inda kuma wani Mai taimakawa gwamna Yana dawainiya da ita har daga karshe ta samu ganin gwamnan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here