Daga Abdulraman Aliyu
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce akalla mutane 1,320 ne aka tabbatar sun mutu a shekaru bakwai da barayin shanu suka kwashe suna kai hare-hare kan kauyukan jihar.
Gwamnatin jihar ta ce an raunata wasu mutane kusan dubu biyu kuma an lalata gidaje da gonaki fiye da dubu goma.
Gwamnatin Tarayyar kasar ta tura runduna sojojin sama zuwa jihar domin taimakawa wajen fatattakar barayin.
Gwamnan Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari ya bayar da umurnin a kashe duk wanda aka gani da bindiga a jihar A wata hira da BBC, sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi ya ce a halin yanzu gwamnatin jihar tana bayar da tallafin kudade da sauran kayayyaki ga wadanda lamarin ya rutsa dasu.
Gwamnatin jihar Zamfara dai ta ce matsalar rikicin masu satar shanu da ke ci gaba da janyo asarar rayuka da dukiyoyi ba za ta rasa nasaba da hannun wasu ba da ba sa son jihar ta zauna lafiya.
Cikin watannin da suka gabata barayin shanu sun yi ta kai hare-haren da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da jikkata wasu.
Ko Bayan kashe shararren narawon nan Buharin Daji, an ci gaba da kai hare-hare a wasu kauyuka na Jihar, wadanda suka haddasa asarar rayuka da dama.