Daga Sulaiman Umar
Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan Sokoto, ya shawarci ‘yan jam’iyyar PDP su kara yawan addu’o’i da tuba ga Allah.
A cewar Bafarawa “Laifukan da ‘yan jam’iyyar PDP suka yiwa Allah ne yasa yanzu yake azabtar da su a hannun APC.
Bafarawa ya yi wannan furuci ne a yayin da yake jawabi a taron Jam’iyyar PDP shiyar arewa maso yamma ranar Asabar a Katsina.
“Allah baya kuskure, sabamar da mukayi ne yasa ya horamu ta hanyar karbar mulki daga hannun mu zuwa hannun APC” cewar Aliyu Sadiq Bafarawa