An Bukaci Sakatarorin Ilimin Katsina Da Su Guji Harkokin Siyasa

0

Daga Sulaiman Umar

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga Sakatarorin Ilimi na kananan hukumomi da kada suyi dumudumu cikin harkokin siyasa domin su tsare martaba da darajar aikin su.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a sa’ilin da ya kaddamar da shirin ciyar da yara ‘yan makarantar Firamare na jihar.

Gwamna Masari ya jaddada cewa wannan Gwamnatin za ta ci gaba da yin duk abinda ya kamata domin tabbatar da an kyautata hanyar koyo da koyarwa a duk makarantun jihar nan, wannan ya sanya ake yin jarabawa a duk lokacin da za a cike gurbin mukamin Sakataren Ilimi.

Ya kuma ja kunnen su da su tabbatar da masu aikin bada abincin suna yin duk abinda ya kamata domin tabbatar da yaran suna samun abincin yadda aka tsara ba tare da algus ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here