Mun amince da kafa sabuwar jami’ar Rundunar Sojoji a Najeriya- Majalisar Ministoci

0

Daga Sulaiman Umar

A zaman da majalisar ministoci ta yi a jiya a karkashin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo, ta amince da kafa wata sabuwar jami’a ta rundunar Sojan Najeriya.

Da yake karin haske kan zaman majalisar, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce za a kafa jami’ar ce a garin Biu da ke jihar Borno. A halin yanzu dai, rundunar tana amfani da kwalejin horas da manyan hafsoshinta da ke Kaduna (NDA) ne wajen bayar da shaidar kammala digiri.

See also  Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Jihar Anambra, Sun Yi Awon Gaba Da Jarirai 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here