ME YA KAI DAMO DA KARE GIDAN GWAMNATIN KATSINA?

0

Daga Wakilin Taskar Labarai

A Kwanakin baya aka fara ganin  sabon tsari na binciken ababen hawa idan sun zo Shiga ko fita daga gidan gwamnatin Jihar  Katsina, abin da ba a ta ba yi ba  a baya.
Wannan yasa Taskar Labarai ta fara binciken me ya kawo hakan? Binciken mu daga wata majiya Mai tushe, wadda Bata so a fadi sunanta ba sun ce  abubuwa biyu suka jawo hakan.

Na daya wasu Jami’an tsaro ne , suka zo ganin gwamnan kuma suka shiga har ciki da makaman su, wanda wannan kamar karan tsaye ne ga tsaro.
Kamata yayi  ko da za su wuce a tabbatar da makaman  a kuma dau matakin hakan.

Na biyu wasu halittu masu kama da Damo ake zargin an shigo dasu, an  sannan aka sake su  a cikin gidan gwamnatin na Katsina, kuma suna yawo.

Majiyar tace ana zargin  kawo wadannan halittu da sakinsu a cikin gidan na gwamnati  yana da alaka da wani kulumboto  ko sihiri.

Majiyar tace akan haka aka dauki matakai daban-daban a gidan daga ciki har da binciken ababen hawa, in sun zo shiga ko fita daga gidan.

Kwanakin baya ma ranar da a kayi taron wata rantsuwa, an ga wani kare na yawo a cikin gidan   wanda kowa ya yi mamaki domin kuwa mazauna gidan sun San cewa duk gidan Babu kare, me ya kawo kare ya a kayi yazo? Ta ina ya shigo?   Abin da aka Dade ke nan ana maganar da kuma tambaya.

Tarihi ya nuna a baya gwamnonin farar hula sun sha fuskantar abin da ake zargi na kulumboto ne ko kuma asiri. Fara daga Sa’idu Barda wanda a lokacin sa aka ce zaman ofis ya gagareshi kullum yana Kaduna daga can ya rika tafiyar da gwamnatinsa.

Malam Umar Musa Yar’adua ma an zargi ya fuskanci wannan Inda akwai lokacin da ya bar kasar neman lafiya ba wanda yayi tsammanin zai dawo, ko kuma Koda ya
dawo ba zai iya komai ba.
Amma cikin ikon  Allah ya yi zangon na farko yayi na biyu har ya dana kujerar shugaban kasa kafin ya rasu.

A kan gwamna Shema kuwa jaridar Almizan ta taba wani labarin cewa ta gano an yi masa wani sammu mai suna Dan madundumi, wanda bai iya gane kuskuren shi, Sai bayan barnar ta faru.
Labarin na jaridar Almizan wanda ya fito a fuskar gaba matsayin babban labari a jaridar. marubucinsa, Danjuma Katsina yayi zurfin bincike harda tattaunawa da wasu malamai a kan sihiri ga shugabanni da kuma sihirin na Dan madundumi.
Wadanda suka San Shema sun ce ga alama lokacin da yana mulkin wannan sammun ya Kama shi sosai.

Kare da kuma Damo   an sake su a gidan gwamnatin Katsina, wa ake zargin zai iya kulumboto? Daga wajen gwamnatin ne? Ko daga cikinta? Na kusa da gwamnan ne masu son mallakarsa, ko na nesa ne masu son shigowa?
An misalata gwamnan Katsina a matsayin mutum mai saukin kai da zuciya mai kyau, da son ya bar tarihi, wanda baya bukatar tara abin duniya.

Amma Inda matsalar take ana zargin wasu na tare dashi suna aikida hallayya da dabi’u na bata masa suna da jawo wa gwamnatin mugun bakin jini, wadansu sunansu yayi kauri ya kuma shahara. Duk Katsina  ana yawan  kama sunan su, ace  sune  kuma sun yi kaza suna kuma yin kaza.

Duk Jin ta bakin Jami’an  gidan gwamnatin Katsina a kan wannan maganar damo da kare taci tura wasu sun ce ai wannan ba maganar ofis bace da ke bukatar wani tabbatarwa ko karyatawa.

Wani kuma cewa yayi, abin da zan ce maka shi ne, Dallatun Katsina na bukatar addu’a shike nan…..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here