Za Mu Mikawa Gwamnati Motoci 48 Da Muka Bankado A Sokoto- Kwastam

0

Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya Kwastam shiyyar jihar Sokoto ta ce ta kama manyan motocin alfarma har guda 48, inda ta ayyana cewa, idan wanda ya mallakesu bai zo ya bayyana ba cikin kwanaki 30 a gaban hukumar ba, za a mika motocin ga gwamnati.

Hukumar kwastam ta ce motocin da ta kama din kirar jip ne.

A lokacin da babban jami’in hukumar na Sokoto, Alhaji Nasir Ahmed ya ke ganawa da manema labarai yau Talata a jihar, ya bukaci jama’a da su dai na alakanta motocin da cewa, na wani dan siyasa ne a jihar  kuma motocin ba guda 160 kamar yadda ake ta yadawa ba.

Nasir Ahmed, ya kara da cewa, mun kama motoci 48 inda har zuwa yanzu bamu sami wanda ya mallake su ba.

An dai sa mu nasarar bankado motocin ne  a wani kango da aka zagaye da Katanga kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here