Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zabi mai magana da yawun kungiyar yakin neman zabensa a karo na biyu.
Shugaba Buhari ya zabi lauya Festus Keyamo (SAN) domin ya zamo mai magana da yawunsa a bangaren yakin nema zabensa na shekarar 2019.
Festus ya tabbatar da zabensa da aka yi a shafinsa na twitter a yau talata, inda yace, nan gaba kadan zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi akan sabon mukamin da ya samu.