An Sace Sandar Majalisar Dokokin Najeriya

0

A yau Larabe ne Majalisar dattawan Najeriya ta ce wasu ‘yan daba sun shiga zauren majalisar inda suka sace sandar majalisar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya fitar, ta yi zargin cewa ‘yan dabar sun shiga majalisar ne karkashin jagorancin Sanata Ovie Omo-Agege, inda suka sace sandar, wadda ita ce alamar da ke nuna kimar majalisar.

Sanarwar ta bayyana wannan al’amari da cin amanar kasa, “don hakan tamkar kokari ne na kawar da wani reshe na gwamnatin tarayya da karfin tuwo, don haka dole a dauki duk matakin da ya dace.

An dai kawo wata sandar ta wucin-gadi an ajiye, kuma majalisar ta bai wa Sufeto Janar na ‘yan sanda da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, su nemo sandar a cikin sa’a 24, sannan su kamo wadanda suka sace sandar.

See also  Malaman Kwalejin Ilimi Ta Bichi Sun Zargi Hukumar Makarantar Da Karkatar Da Naira Milyan 34

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here