Rundunar ‘yan sandan Najeiya ta kama Sanata Ovie Omo-Agege, a harabar majalisar dokokin kasar, wanda take zarginsa da tura ‘yan daba don sace sandar majalisar dattawa da aka yi.
An sace sandar majalisar ne da safiyar yau Laraba yayin da wasu da majalisar ta yi zargin ‘yan daba ne karkashin jagorancin Sanata Omo-Agege, wanda aka dakatar da shi a makon da ya wuce, suka kutsa zauren majalisar lokacin da ake zama, suka ‘sace’ sandar majalisar.
Sai dai har i zuwa yanzu Sanata Omo-Agege, bai ce komai ba game da zargin da majalisar ta yi masa na shiga da ‘yan daban da ya yi.