An Gano Sandar Majalisa Dattawa Da Aka Sace

0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta gano sandar girmar Majalisar da wasu ‘yan daba suka sace a jiya Laraba.

Haka kuma rundunar ta ce an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen Majalisar dokokin tarayyar kasar don dakile afkuwar hakan.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Aremu Adeniran ya aikewa manema labaru a yau alhamis.

Sanarwar ta ce an gano sandar ne a wani wuri da ke kusa da gadar kofar shigowa gari wato City Gate da ke Abuja.

Rundunar ta kara da cewa wadanda suka sace sandar sun jefar da ita ne sakamakon tsaurara matakan tsaro da ‘yan sanda suka yi a garin Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here