An Tsinci Gawar ‘Yar Shekara Uku Da Aka Yi Wa Fyade A Kano

0

Hukumar ‘Yan sanda a jihar Kano, kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar SP Magaji Musa Majiya ya bayyana wa manema labarai  cewa, sun kama malaman wata makaranta su tara bayan da aka samu gawar wata yarinya ‘yar shekara uku da aka yi wa fyade.

An dai gano gawar yarinyar ne a cikin ajin makarantar kwanaki hudu bayan da iyayenta suka sanar da bacewar ‘yarsu.

An ce dai an gano gawar, wadda har ta fara rubewa kwance a cikin jini kuma tsirara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here