Shugaba Buhari yana magana ne a taron kasashen renon Ingila dake gudana a birnin Landan.
Sai dai kalaman sa na ci gaba da tayar da kura a tsakanin matasan kasar musamman a kafafen sada zumunta na zamani.
Matasa da dama dai sun nuna damuwarsu kan kalaman da suka ce na zubar da kima ne, da shugaban ya yi.
Jim kadan, mai bai wa shugaban shawara kan kafafen watsa labarai Sha’aban Sharada, ya ce matasa da dama ba su fahimci kalaman Shugaba Buhari ba.