A karshe dai yau Litinin, rundunar ‘yan sanda ta samu nasarar cafke dan majalisar Dattawan nan mai wakiltar Jihar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Maleye bisa zargin daukar nauyin ayyukan ta’addanci a jiharsa.
Sanata Melaye ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter cewa an kama shi ne da safiyar ranar Litinin a filin jirgin sama na Abuja.
Sanatan ya kara da cewa “an kama shi ne bayan ya wuce shingayen bincike na jami’an tsaro domin tafiyar aiki zuwa kasar Morocco”.
Kawo yanzu babu bayani daga hukumomin tsaro kan batun kama Sanata Melaye.