A yau talata akalla mutum 17 ne suka rasa rayukansu, tare da wasu limaman coci biyu, bayan wani hari da aka kai wata cocin darikar katolika watau St Ignatius Catholic Church a jihar Benue kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.
Wadansu mahara ne wadanda gwamnatin jihar ta ce makiyaya ne suka kaddamar da harin a garin Ayar-Mbalom da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas.
Kuma cikin mutanen da aka kashe har da limaman coci guda biyu.
Duk dakai harin maharan sun kona akalla gidaje kimanin 50, a cewar gwamnatin jihar ta bakin mai magana na yawun jihar Terver Akase.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan, gami da mika jaje ga gwamnati da al’ummar jihar.