Dan majalisar dokokin jihar Zamfara Honarabul Dan Bala Yarkufoji ya rasa iyalanshi su goma sakamakon hadarin mota daga Gusau zuwa Bakura.
An dai yi jana’izar su kamar yadda addinin musulunci ya shardanta.
Daga cikin iyalan dan majalisar wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar hadarin motar, akwai ya’yanshi 3 da kuma jikokinshi 4 da yar’uwarshi da kuma kanwar matarshi sai direban nasu.
Jama’a da dama suka samu halartar jana’izar har da gwamnan jihar ta Zamfara Abdul-aziz Yari da kuma mataimakishi, Malam Ibrahim Wakkala.
A cewar Jami’in hulda da jama’a na Majalisar dokokin jihar Zamfara, Malam Nasiru Usman Beriki, ya ce hadarin ya faru ne bayan sun isa garin Gusau domin hidimar auren daya daga cikin ‘yayan Hon Saidu.
“Bisa hanyarsu ta komawa gida ne bayan sun bar Gusau, sun wuce Bungudu, sun kai gadar da ke fita garin Bungudu, suka hadu da wata babbar mota wadda ta ke dauke da kwalaben lemu”, in ji shi.